Zaben Shugaban Ƙasar Ghana Ya Sa PDP Ta Hango Abin da Zai Faru da Tinubu a 2027
- Jam'iyyar PDP ta taya mutanen Ghana murnar zaɓen jagoran ƴan adawa kuma tsohon shugaban ƙasa, John Mahama a zaɓen ranar Asabar
- Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba ya ce nasarar ƴan adawa a Ghana alama ce da ke nuna ƙarshen APC ya kusa a Najeriya
- PDP ta roki hukumar zaɓe da jami'an tsaro su tabbatar da muradin ƴan Najeriya na kawo ƙarshen mulkin danniya a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam’iyyar PDP ta taya al’ummar kasar Ghana murnar jajircewa da suka yi wajen kare dimokuradiyya tare da tabbatar da sun zabi wanda suke so ranar Asabar.
A ranar Asabar da ta gabata ne al'ummar ƙasar Ghana suka zaɓi jagoran ƴan adawa na jam'iyyar NDC, John Mahama a matsayin shugaban ƙasa.
PDP ta taya su murna bisa wannan jajircewa da suka yi a zaɓen a wata sanarwa da jam'iyyar ta wallafa a shafin X ɗauke da sa hannun kakakinta, Debo Ologunagba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaɓen Ghana: PDP ta hango nasara a 2027
Debo Ologunagba ya bayyana cewa nasarar ƴan adawa a ƙasar Ghana babbar alama ce da ke nuna karshen mulkin Bola Tinubu da APC ya zo ƙarshe a Najeriya.
Ya ce:
"Matakin da al'ummar Ghana suka ɗauka a zaɓen shugaban ƙasa alama ce da ke nuna cewa kwanan APC ya kusa ƙarewa a kan gadon mulkin Najeriya.
"Kamar ƙasar Ghana, za a kawo karshen mulkin danniya na APC, Najeriya za ta dawo kan turbar shugabanci na gari, za a samu tsaro da bunkasar tattalin arziki ƙarƙashin PDP a 2027."
Jam'iyyar PDP ta buƙaci INEC ta yi adalci
PDP ta ƙara da cewa abin da takaice a shekara tara da rabi da suka wuce, APC ta riguza Najeriya da matsalar tsaro wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 65,000.
Ta yi kira ga hukumomin gwamnati musamman hukumar zaɓe INEC da jami'an tsaro su tabbatar da mutane sun zabi wanda suke so a zaɓuka masu zuwa.
Akume yana so Atiku su hakura da neman mulki
A wani labarin, kun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya nemi ƴan siyasan Arewa su haƙura da neman kujerar shugaban ƙasa a 2027.
Sanata Akume ya ce wannan lokacin ƴan kudu ne, don haka ya kamata a bar shugaba Bola Tinubu ya kammala shekaru takwas a kan madafun iko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng