Gwamna Ya Buɗe Ƙofar Haɗa Kai da Wasu Jam'iyyun Siyasa gabanin Zaben 2027
- Gwamna Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ƙofar APGA a buɗe take ga kowace jam'iyya mai aƙidar ci gaban kasar nan
- Charles Soludo ya bayyana hakan ne a wurin taron kwamitin zartarwa watau NEC na APGA ta ƙasa ranar Juma'a a Abuja
- Gwamnan ya ce a shirye suke su haɗa karfi da karfe da kowace jam'iyya domin kai Najeriya tudun mun tsira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnan Anambra kuma jagoran APGA na kasa, Farfesa Charles Soludo ya bayyana cewa jam’iyyar a shirye take ta ƙuƙƙa ƙawance kowace jam’iyyar siyasa.
Gwamna Soludo ya ce kofar APGA a buɗe take kuma a shirye take ta haɗa kai da kowace jam'iyyar siyasa matuƙar tana da burin kawo sauyi da ci gaba a ƙasar nan.
Soludo ya faɗi haka ne ranar Juma’a a Abuja a taron kwamitin zartarwa watau NEC ta jam'iyyar APGA, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya ce ƙofar APGA a buɗe take
Charles Soludo ya kuma jaddada cewa jam'iyyar APGA ita ce ta farko mai aƙidar kawo ci gaba a Najeriya.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN ya ce bayan warware duk wata taƙaddama da ta dabaibaye APGA da hukuncin kotun koli, a yanzu jam'iyyar ta shirya.
Ya bukaci sauran jam’iyyun siyasa masu son ci gaba a kasar nan da su hada kai da APGA domin ɗaga ƙimar Najeriya, Vanguard ta ruwaito.
APGA ta shirya haɗa maja don ceto Najeriya
“APGA a shirye take ta ƙulla ƙawance da duk jam’iyyar da ke da ra’ayi da akidar ci gaba na gaskiya domin hada karfi da karfe wajen sake gina Najeriya.
"Ni dai a wurina mun shirya gayawa duniya APGA na nan da ranta, APGA tana da karfi, APGA na ƙara yaɗuwa da karbuwa, shi ya sa muka taru domin aika wannan sako a yau.
"APGA ce jam'iyya ta farko mai aƙidar kawo ci gaba, wadda ta yi rijista a hukumance a 2002, duk wata jam'iyyar ci gaba da ta zo mun riga ta, mune na farko a ƙasar nan."
- Charles Soludo.
Gwamna Soludo ya fara biyan sabon albashi
Kun ji cewa Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya tabbatar da fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000 tun a watan Oktoba.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Dr. Law Mefor ya ce rahoton da ake yaɗawa cewa Anambra ba ta cikin jihohin da suka yi ƙarin albashi ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng