Bayan Sauya Sheƙar Ɗiyar Tsohon Gwamna, PDP Ta Kori Ɗan Majalisar Tarayya Nan Take
- Jam'iyyar PDP ta sallami ɗan Majalisar wakilai daga jihar Imo, Hon. Ikenga Imo Ugochinye bisa zargin rashin ɗa'a da zagon ƙasa
- Sakataren PDP ns jihar Imo, Lancelot Obiak ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a
- Ya ce PDP reshen ƙaramar hukumar Ideato ne ta kori ɗan majalisar bayan kammala bincike kan zargin da ake masa ranar Alhamis da ta wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Imo - Jam'iyyar adawa PDP ta kori ɗan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Ideato ta Arewa/Ideato ta Kudu a jihar Imo, Ikenga Imo Ugochinye.
PDP ta sallami ɗan majalisar daga inuwarta ne kan zargin rashin ɗa'a, rashin adabi da biyayya da kuma cin amanar jam'iyya.
Mai magana da yawun PDP reshen jihar Imo, Lancelot Obiak shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 6 ga watan Disambar 2024, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta kori ɗan Majalissr Tarayya
Ya ce shugabannin PDP na karamar hukumar Ideato ne suka kori ɗan majalisar a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Disamba.
Wasiƙar na ɗauke da sa hannun shugaban jam'iyya na Ideato, ThankGod Okeke da sakatarensa, Onyebuchi Umeh kuma sun saka adireshin shugaban PDP na jihar Imo.
Mai magana da yawun PDP ya ce an kori Hon. Ikenga bayan kwamitin ladabtarwa ya miƙa rahoton binciken da ya yi kan zargin da ake masa.
Dalilin korar ɗan Majalisar Wakilai daga PDP
Tun farko dai jam'iyyar PDP ta dakatar da ɗan Majalisar wakilan a matakin gundumarsa bayan ya ƙi mutunta gayyatar da aka masa ranar 14 ga watan Oktoba.
A rahoton Channels tv, wani sashin sanarwar ta ce:
"Kwamitin zartarwa na PDP a karamar hukumar Ideato ta Arewa ya yi taro ranar 5 ga Disamba, 2024, kuma ya amince da rahoton kwamitin ladabtarwa”.
"Don haka mun kori Hon. Ikenga Imo Ikeagwonu daga PDP nan take, kuma daga yau shi ba ɗan jam'iyya ba ne a gundumar Umuopia/Umukegwu."
Wani matashin ɗan siyasa kuma ɗan PDP a Katsina, Kabir Abdullahi ya faɗawa Legit Hausa cewa jam'iyyar ba ta bukatar korar wasu a halin da take ciki.
A cewarsa, kamata ya yi shugabannin PDP su maida hankali wajen haɗa kan ƴaƴan jam'iyyar maimakon korar waɗanda ke cikin gwamnati.
"Wannan kuskure ne amma na ga uwar jam'iyya ta ƙasa ta soke matakin, duk da haka ban ga dalilin korar ɗan majalisa a halin da PDP ke ciki ba," in ji shi.
Ɗiyar tsohon gwamna ya bar PDP zuwa APC
Rahoto ya gabata cewa ƴar Majalisar wakilai daga jihar Delta kuma ɗiyar tsohon gwamna ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Misis Ibori-Suenu ta sanar da sauya shekarta hukumance a wata wasika da ta aikewa shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Asali: Legit.ng