PDP: 'Yar Majalisar Tarayya da Ta Koma Jam'iyyar APC Ta Rasa Kujerarta

PDP: 'Yar Majalisar Tarayya da Ta Koma Jam'iyyar APC Ta Rasa Kujerarta

  • Jam'iyyar PDP ta ayyana kujerar Hon. Erhiatake Ibori-Suenu babu kowa bayan ta koma APC mai mulkin Najeriya
  • Jam'iyyar ta dauki matakin ne kan yar tsohon gwamnan Delta, James Ibori domin hukumar INEC ta sake gudanar da wani zabe
  • Hakan ya biyo bayan sanarwar da Erhiatake ta fitar da take sanar da ficewarta daga PDP saboda rikice-rikice

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ayyana kujerar yar Majalisar Tarayya da ta koma APC babu kowa.

Jam'iyyar PDP ta dauki matakin ne kan ‘yar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori mai suna Hon. Erhiatake Ibori-Suenu bayan ta sauya sheka zuwa APC.

PDP ta ayyana kujeraryar Majalisa babu kowa
Jam'iyyar PDP ta ce babu kowa a kujerar yar Majalisar Tarayya nda ta bukaci sake zabe. Hoto: People's Democratic Party, PDP.
Asali: Facebook

Dalilan Ibori-Suenu na barin PDP zuwa APC

Jam'iyyar ta tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook a jiya Juma'a 6 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

"Ban saɓawa Doka ba," Ƴar Majalisar Tarayya ta faɗi dalilinta na fita daga PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba Ibori-Suenu wacce ke wakiltar mazabar Ethiope ta Tarayya a jihar Delta ta watsar da PDP tare da komawa APC.

Ibori-Suenu ta bayyana matakin nata a cikin wata wasika da ta rubutawa shugaban PDP na karamar hukumar Ethiope West.

A cikin sanarwar, Ibori-Suenu ta ce ficewar tata na da nasaba da rikice-rikicen jam'iyyar da rashin shigar da ita cikin harkokin jam’iyyar a matakin jiha.

PDP ta ayyana kujerar Ibori-Suenu babu kowa

A cikin sanarwar, kakakin yada labaran jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya bukaci hukumar INEC da ta yi gaggawar gudanar da zabe.

Ologunagba ya fara shirye-shiryen gudanar da zaben zai taimaka wurin cike gurbin kujerar da aka ayyana babu kowa.

Jam’iyyar ta bukaci Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gaggauta fara shirye-shiryen gudanar da sabon zaɓe domin cike gurbin kujerar.

Dan PDP ya yi magana da Legit Hausa kan lamarin

Kara karanta wannan

Kwamitin APC ya fara zaman sulhu, an dauko hanyar sasanta 'yan jam'iyya

Kwamred Abubakar Abdulkadir ya nuna damuwa kan matakin PDP inda ya ce ko kadan ba ta saba doka ba.

"Kamar yadda ta bayyana ta bi duka tsarin doka kafin ɗaukar wannan mataki kuma yan jam'iyyu da dama sun bar na su jam'iyyar zuwa PDP."

- Kwamred Abdulkadir

Dan a mutum PDP ya ce a siyasar Najeriya sauya sheka ya zama ruwan dare kamar yadda ta fita wasu za su shigo.

PDP ta fara neman hanayar warware matasalolinta

Kun ji cewa Kwamitin amintattu na PDP (BoT) ya taso shugabannin jam'iyyar a gaba kan cigaba da ɗage taron NEC.

Shugaban kwamitin amintattun ya buƙaci shugabannin na PDP da su tabbatar sun gudanar da taron NEC a watan Faburairun 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.