Gwamna Ya Yi Rabon Mukamai, Ya Jawo Matasan APC 200 cikin Gwamnati

Gwamna Ya Yi Rabon Mukamai, Ya Jawo Matasan APC 200 cikin Gwamnati

  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya jawo matasan jam'iyyar APC domin shigowa a dama da su a cikin gwamnatinsa
  • Nasir Idris ya gwangwaje matasan jam'iyyar APC 200 da muƙaman masu taimaka masa na musamman
  • Shugaban APC na jihar, Abubakar Kana-Zuru ya yaba da ayyukan da Gwamna ya gudanar tun bayansa kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi rabon muƙamai ga matasan jam'iyyar APC.

Gwamna Nasir Idris ya naɗa matasa 200 na jam'iyyar APC a matsayin mataimakansa na musamman.

Gwamnan Kebbi ya yi rabon mukamai
Gwamna Nasir Idris ya ba matasan APC mukamai Hoto: @NasirIdrisKIG
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta ce naɗin wanda ya ƙunshi maza da mata, shugaban APC na jihar, Abubakar Kana-Zuru ne ya gabatar da shi a sakatariyar jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban APC ya yabawa Gwamna Nasir

Ya bayyana jin daɗinsa da shugabancin gwamnan, inda ya bayyana cewa, a lokacin yaƙin neman zaɓe, ƴan jam’iyyar APC sun ratsa kowane lungu da saƙo na jihar domin neman ƙuri'un zaɓe, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Wasu ƙarin yan Majalisar Tarayya na shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki'

Ya kuma yabawa gwamnan bisa cika kaso 80% cikin 100% na alƙawurran da ya ɗaukarwa al’ummar jihar.

Daga cikin muhimman nasarorin da gwamnan ya samu waɗanda Abubakar Kana-Zuru ya bayyana suna haɗa da, saye da rarraba takin zamani kyauta ga manoma, da kuma rarraba kayan abinci ga jama'a.

Sauran nasarorin da aka samu sun haɗa da gina tituna tare da samar da fitulu masu amfani da hasken rana a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, da kuma kammala sakatariyar zamani ta biliyoyin naira.

Mutanen Kebbi na jin daɗin gwamnan

Shugabar matan APC a jihar, Aisha Gulabi, ta yabi da halin kirkin gwamnan.

"Mu mutanen Kebbi mun ji daɗi. Allah ya albarkace mu da gwamna mai kyautatawa mai kyautata masa da wanda ya yi masa abu mara kyau."

- Aisha Gulabi

Gwamnan Kebbi ya ba sarakuna motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ba da sababbin motoci ga sarakuna huɗu domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Gwamna Nasir Idris ya ba kowane sarki daga cikin sarakuna guda huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar Kebbi motar Toyota Land Cruiser a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng