'Babban Dalilin da Ya Sa Ƴan Majalisar Tarayya 4 Suka Sauya Sheka zuwa APC'

'Babban Dalilin da Ya Sa Ƴan Majalisar Tarayya 4 Suka Sauya Sheka zuwa APC'

  • Hon. Benedict Etanabene ya bayyana cewa ƴan majalisar tarayya na LP sun koma APC ne domin fara shirin zaɓen 2027
  • Ɗan majalisar wakilan wanda ya fito daga jihar Delta ya ce babu abin da zai sa ya bar jam'iyyar LP zuwa wata daban
  • Ya ce a halin da ake ciki kuri'un jama'a ba su da amfani a kowane irin zaɓe a Najeriya, ya yi kira ga mahukunta su canza tsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya, Benedict Etanabene, ya soki matakin da wasu ƴan jam'iyyarsa ta LP suka ɗauka na komawa APC mai mulki.

Hon. Etanabene mai wakiltar mazaɓar Okpe/Sapele/Uvwie a jihar Delta, ya ce ƴan majalisar LP huɗu da suka koma APC sun yi haka ne saboda shirin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ban mamaki, sun kashe wata ƴar Kasuwa da malamin addini

Benedict Etanabene.
Dan Majalisa ya gano dalilin sauya shekar abokan aikinsa zuwa APC Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Juma'a, 6 ga watan Disamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ƴan majalisa 4 na komawa APC

Ya ce ƴan majalisar tarayya da suka sauya shekar sun duba sakamakon zaben da aka yi kwanan nan a jihohin Edo da Ondo, wanda ƴan takarar APC suka samu nasara.

Etanabene ya ce:

"Babu wani rikicin shugabanci a jam'iyyar LP, idan ma akwai rikicin ina da tabbacin galibin waɗanda suka sauya sheka duk suna goyon bayan shugabancin Julius Abure ne."
"Abin da ya faru a jihohin Edo da Ondo abin tsoro ne domin da alama ko a zaɓen 2027 APC za ta yi kasuwanci ne kamar yadda ta saba, ina ga hakan ya sa ƴan majalisar suka ga bari su shiga tun yanzu."

"Ba zan taɓa barin LP ba" - Etanabene

Da aka tambaye shi ko hakan barazana ce gare shi a 2027, dan majalisar ya ce babu abin da zai sa ya bar jam’iyyar LP zuwa wata jam’iyya daban.

Kara karanta wannan

Bayan ficewar 'dan takarar gwamna, 'yan majalisun LP sun koma jam'iyyar APC

Benedict Etanabene ya koka kan cewa ƙuri'un da ƴan Najeriya suke kaɗawa a rumfunam zaɓe ba za su ake ƙidayawa ba, ya bukaci a gaggauta canza tsarin.

Ɗiyar tsohon gwamna ta koma APC

Rahoto ya gabata cewa ƴar majalisar wakilan tarayya daga jihar Delta, Erhriatake Ibori-Suenu ta sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Erhriatake Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamna, James Ibori ta sanar da haka ne a wasiƙar da ta miƙawa kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262