Kwamitin APC Ya Fara Zaman Sulhu, An Dauko Hanyar Sasanta 'Yan Jam'iyya
- Jam'iyyar APC ta fara kokarin hade kan jam'iyyarta a Adamawa domin gyara siyasarta a shekarar 2027 da za a yi zabe
- Kwamitin mutane takwas ne su ka zauna a Adamawa, daga ciki har da Sanatoci da manyan 'yan siyasan da ake ji da su
- Sanata Mohammed Mohammed Mana, a zantawarsa da manema labarai ya bayyana cewa sun kammala shirin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Adamawa - APC ta bayyana cewa akwai shirin da ta ke yi na tabbatar da cewa ta kwace Adamawa daga jam’iyyar adawa ta PDP.
An bayyana haka ne bayan kwamitin sasancin APC a jihar ya zauna domin warware kalubalen da ta ke fuskanta a Adamawa.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewar kwamitin ya bayyana cewa sun a kulla babban shiri a kan jihar gabanin zaben 2027 mai gabatawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar APC na shirin mamaye Adamawa
A dazu ne jaridar Blueprint ta wallafa cewa kusoshin APC sun yi ganawar sirri domin gano yadda za su warware kalubalen da ke damunsu.
A zantawarsa da manema labarai bayan zaman, Mohammed Mana ya ce sun daura damarar gyara tafiyarsu domin yin nasara a jihar.
Kwamitin sulhun APC ya zauna a Adamawa
Kwamitin sulhu na mutum takwas a Adamawa ya hada da Sanatoci kamar Bello Tukur, Abubakar Girei, Binta Masi.
Sauran sun hada da Hon. Yusuf Buba Yakubu, Dr Bridget Zidon da Isa Baba wanda ya zama sakataren kwamitin.
A cewar Sanata Mohammed Mana'
“Adamawa jiha ce mai muhimmanci, kuma mun kuduri aniyar ganin APC ta samu mafi yawan kujeru a 2027. Za mu kai ga wadanda suka ji an bar su a baya a lokacin zabukan fidda gwani da na gaba domin hadin kan jam’iyyar karkashin tutar APC.
Adamawa: Rikicin APC ya yi kamari
A baya kun ji cewa rikicin jam'iyya mai mulki ta APC ya kara kamari a jihar Adamawa, har ta kai ga an kafa kwamitin sulhu na mutane takwas domin daidaita al'amura.
Kwamitin zai gudanar da taro a Yola karkashin jagorancin mataimakin shugaban APC na Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu da zummar warware matsalolin da ake fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng