'Yan Majalisar Amintattun Jam'iyyar PDP Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja
- Ƴan majalisar amintattun jam'iyyar PDP watau BoT sun shiga taron gaggawa a Abuja yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, 2024
- Majalisar BoT-PDP ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara ta shiga wannan ganawa ne kan wasu muhmman batutuwa da suka shafi jam'iyyar
- Duk da ba bayyana ajandar wannan zama ba, ana ganin BoT za ta maida hankali ne kan rigingimun cikin gida da taron kwamitin zartarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar amintattun jam'iyyar PDP ta ƙasa watau BoT ta shiga taron gaggawa yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan majalisar ba su bayyana ainihin abin da za su tattauna a wannan taro na yau Alhamis, 5 ga watan Disamba, 2024 ba.
BoT-PDP ta shiga taron gaggawa a Abuja
Sai dai a cewar rahoton jaridar Vanguard, duk da ba a faɗi ajendar taro na gaggawa ba, ana ganin ƴan BoT za su fi maida hankali ne kan harkokin cikin gida na PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa ƴan majalisar amintattun za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi PDP ciki har da taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC da ke tafe.
Majalisar amintattun PDP ta soki ɗage taron NEC
Bayan kammala taron, majalisar BoT ta caccaki kwamitin gudanarwa na PDP karkashin jagorancin Umar Damagum bisa sake ɗage taron kwamitin NEC.
Shugaban BoT, Sanata Adolphus Wabara ya ce majalisa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba har sai ta ga bayan rigingimun cikin gida da suka hana PDP rawar gaban hantsi.
Ya bayyana cewa majalisar amintattun ta shirya zama da tsohon gwamnan Ribas kuma ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike a watan Janairu, 2025, cewar rahoton Punch.
BoT ta shirya kawo karshen rikicin PDP
Wabara ya jaddada cewa karfin jam’iyyar PDP ya ta’allaka ne a kan hadin kai tsakanin yaƴanta da kuma tsayawa kan tsarin dimokuradiyya.
Ya kara da cewa kwamitin NEC shi ne mafi ƙololuwa da ake zama don ɗaukar mataki, tuntuɓar juna da haɗa kai tsakanin shugannin PDP na kowane mataki.
Tsohon minista ya fice daga jam'iyyar PDP
Rahoto ya gabata cewa a lokacin da jiga-jigan PDP ke faɗi tashin lalubo bakin zaren a rikicin cikin gida, tsohon minista ya fice daga jam'iyyar.
Osita Chidoka, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya tabbatar da barin PDP ne a wata wasiƙa da ya miƙawa shugabannin jam'iyya na gundumarsa a Anambra.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng