Bayan Ficewar 'Dan Takarar Gwamna, 'Yan Majalisun LP Sun Koma Jam'iyyar APC

Bayan Ficewar 'Dan Takarar Gwamna, 'Yan Majalisun LP Sun Koma Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar LP ta rasa wasu daga cikin ƴan majalisunta na majalisar wakilai bayan sun sanar ficewarsu daga cikinta
  • Ƴan majalisun guda huɗu da suka fito daga jihohi daban-daban sun sanar da sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Ɗaya daga cikinsu mai wakiltar mazaɓar Kaura a Kaduna, Donatus Matthew ya ce sun koma APC bayan sun gamsu da su yi hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan majalisar wakilai da aka zaba a inuwar jam'iyyar LP, sun sauya sheƙa zuwa APC.

Ƴan majalisun huɗu sun sanar da sauya sheƙarsu ne zuwa APC a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2024.

'Yan majalisun LP sun koma APC
'Yan majalisar wakilai na jam'iyyar LP sun koma APC Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce ƴan majalisun da suka bar LP zuwa APC sun haɗa da Tochukwu Okere (Imo) da Donatus Mathew (Kaduna).

Kara karanta wannan

PDP ta kara babban rashi, yar tsohon gwamna da ke majalisa ta sauya sheƙa zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan akwai Bassey Akiba (Cross River), Iyawe Esosa (Edo) da kuma Daulyop Fom (Plateau).

Meyasa ƴan majalisar LP suka koma APC?

Da yake tabbatar da hakan, Donatus Matthew, mai wakiltar Kaura daga jihar Kaduna, ya ce sun koma APC ne bayan sun gamsu da su yi hakan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Ba za ka yi aiki da abin da mutanen da ke mazaɓarka za su yanke ba, saboda mutane suna da yadda suke fahimtar abubuwa daban-daban."
"Na ɗauki wannan matakin ne bisa gamsuwa da hakan. Wannan ya sanya ko ka ƙi ko ka so, akwai mutanen da ke mazaɓata waɗanda suka gamsu cewa sauya sheƙar shi ne abin da ya dace a wajensu."
"Akwai kuma masu yin ɗar-ɗar waɗanda suke jira su ga abin da zai faru."

- Donathus Matthew

Shugaban majalisa ya tabbatar da sauya shekar

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, shi ne ya karanta wasiƙar sauya sheƙar ta su a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

DHQ ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu kan 'yan ta'adda a cikin shekara 1

Sauya sheƙar ta su dai na zuwa ne bayan ɗan takarar gwamnan Edo na jam'iyyar LP, Keneth Imansuangbon ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Ndume ya yi barazanar barin jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana cewa a shirye yake ya raba gari da jam'iyyar APC.

Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya nuna cewa zai bar APC idan har shugabanninta suka ba shi damar yin hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng