Ministan Tinubu Ya Rasa, Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Dan Majalisar Tarayya a PDP

Ministan Tinubu Ya Rasa, Kotu Ta Yi Hukunci kan Dakatar da Dan Majalisar Tarayya a PDP

  • Watanni bakwai bayan dakatar da dan Majalisar Tarayya daga jam'iyyar PDP, Babbar Kotun jihar Rivers ta yi hukunci kan matakin
  • Kotun da ke birnin Port Harcourt da rusa matakin dakatar da dan majalisar mai wakiltar mazabar Andoni-Opobo/Nkoro mai suna Awaji-Inombek Abiante
  • Tsagin jam'iyyar PDP da ke tare da Nyesom Wike ya dakatar da Abiante a watan Mayun 2024 kan zargin rarraba kawunan yan jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Babar Kotun jihar Rivers da ke Port Harcourt ta yi hukunci kan matakin da jam'iyyar PDP ta dauka kan wani dan Majalisar Tarayya.

Kotun ta rusa dakatarwar da aka yi wa dan Majalisar mai wakiltar mazabar Tarayya ta Andoni-Opobo/Nkoro, Awaji-Inombek Abiante.

Kotu ta yi hukunci kan dakatar da dan Majalisar Tarayya da PDP ta yi
Kotu a Rivers ta rusa dakatar da dan Majalisar Tarayya da PDP ta yi. Hoto: @RepAbianteD.
Asali: Twitter

Kotu ta rusa dakatar da dan majalisar PDP

Channels TV ta ruwaito cewa tsagin shugabannin jam'iyyar a yankin ne suka dakatar da dan Majalisar a watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Kalubalen APC na kara kamari, wasu sun balle don kafa sabuwar jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce dakatar da Abiante daga jam’iyyar PDP da cewa bai halatta ba kuma hakan ya saba saba doka, cewar Punch.

Abiante ya kasance na hannun daman Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers inda ake zargin wadanda suka dakatar da shi na tare da Ministan, Abuja Nyesom Wike.

Zargin da ake yi wa dan Majalisar

Tsagin jam'iyyar karkashin jagorancin Dike Bara tare da wasu mutane 13 sun sanar da dakatar da Abiante bisa zargin yin ayyukan da suka sabawa jam’iyya.

Har ila yau, ana zargin cewa dan Majalisar yana karfafa bangaranci a matakin mazaba da kuma yana goyon bayan wata kungiya karkashin sunan jam’iyyar.

Jonathan ya yabawa Gwamna Fubara a Rivers

Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sha ruwan yabo daga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Jonathan ya ce Gwamna Fubara ya jajirce wurin tabbatar da samun cigaba a jihar Rivers da kuma yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Kara karanta wannan

Tinubu: 'Yan majalisun Arewa sun sa an dakatar da muhawara kan kudirin haraji

Tsohon shugaban kasar ya bayyana Gwamna Fubara a matsayin 'Janar' a bangaren siyasa ya ce ya yi gwagwarmaya sosai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.