Jerin Gwamnoni da Manyan Ƴan Siyasar Arewa da Suka Ɗauki Zafi kan Kudirin Harajin Tinubu

Jerin Gwamnoni da Manyan Ƴan Siyasar Arewa da Suka Ɗauki Zafi kan Kudirin Harajin Tinubu

Abuja - Kudirori huɗu na sauya fasalin haraji da mai girma shugaban kasa, Bola Tinubu ya mikawa Majalisar Tarayya bai yi wa manyan Arewa daɗi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƴan Arewa da suka haɗa da gwamnoni, jiga-jigan siyasa, sarakuna da ƴan majalisu sun yi fatali da kudirin wanda suke zargin za a durƙusar da yankinsu.

Atiku, Tinubu da Zulum.
Yan siyasan Arewa da suka fi daukar zafi a kan kudirin haraji a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Professor Babagana Umar Zulum
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa dai sun bukaci shugaban ƙasa ya janye kudirin harajin domin ba da ƙofar sake tattaunawa a kansa a fahimci juna, rahoton Punch.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku gwamnoni da ƴan siyasar Arewa da suka ɗauki ɗumi kan sabon kudin sauya fasalin haraji na Shugaba Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Gwamna Zulum ya yi fatali da kudirin haraji

Gwamna Borno, Babagana Zulum ya ce duk da cewa Tinubu na da ikon aiwatar da ƙudirin haraji, amma yin hakan na iya haifar gagarumar illa ga miliyoyin ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Hayaniya ta ɓarke a Majalisar Wakilai kan ƙudirin sauya fasalin harajin Tinubu

Babagana Zulum ya ce sabuwar dokar ba alheri ba ce ga jihohin Arewa da wasu jihohin Kudu, yana mai nuna adawarsa da dokar a fili.

A wata hira da ya yi da Channels tv, gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya ta janye kudirin, a sake zama a tattauna kuma a nemi shawarwari.

"Menene na gaggawar kai kudirin majalisa? Mun bukaci gwamnatin tarayya ta dakata, ta cire wasu tsaruka da za su illata Arewa. A kididdigarmu jihohin Legas da Ribas ne za su amfana," in ji Zulum.

2. Matsayar Gwamnan Bala Mohammed

Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba kudirin gyara harajin da ke gaban majalisa.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Gwamna Bala ya bukaci Tinubu ya dakatar da kudirin kuma ya faɗaɗa neman shawari domin tabbatar da adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: An fara samun rabuwar kai tsakanin gwamnonin Arewa

Ya ce akwai buƙatar sake nazari kan kudirorin tare da maida hankali kan haɗin kan ƙasa maimakon a nemi kawo rarrabuwar kai.

3. Gwamna Sule ya magantu kan kudirin haraji

Gwamma Abdullahi Sule na jihar Nasarawa na daga cikin waɗanda suka fito ƙarara suka nuna adawa ga kudirin sauya fasalin harajin shugaba Tinubu.

Sule ya ce ko kaɗan matsayar da suka ɗauka ba ta da alaƙa da juyawa shugaban ƙasa baya, burinsu kawai a dawo a sake lale tun daga farko kafin miƙa kudirin majalisa.

A rahoton da The Nation ta wallafa a kwanakin baya, Abdullahi Sule ya bayyana cewa suna bukatar shugaba Bola Tinubu ya yi sauyi ga kudirin kafin su amince da shi.

4. Atiku ya sa baki a kudirin haraji

A nasa ɓangaren, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce bai kamata a lalata tsarin kasafta kudi tun daga matakin tarayya ta hanyar fifita wasu jihohi ba.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa gwamnonin Najeriya suka bukaci Tinubu ya janye ƙudirin haraji'

Bisa haka, Atiku ya yi kira da a tabbatar da adalci da daidaito yayin tattaunawa kan kudirin sauya fasalin haraji da ke gaban majalisar tarayya yanzu haka.

A maganar da ya wallafa a shafin X, Wazirin Adamawa ya ce ya kamata majalisa ta yi taka tsan-tsan kuma ta tabbatar da cewa kudirin ya yi daidai da muradan ƴan Najeriya.

5. Ali Ndume ya soki gyaran tsarin

Sanata Ali Ndume (APC, Borno ta Kudu) ya bayyana cewa ba zai goyi bayan bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sauya fasalin haraji ba.

Ndume ya ce a halin yanzu mutane na fafutukar neman abin da za su ci ne saboda masifar tsadar rayuwa, don haka ya kamata gwamnatin Tinubu ta tausaya musu.

Sanatan, wanda ke shan yabo daga ƴan Arewa, ya tsaya kai da fata a zauren majalisar dattawa, yana mai nuna illar kudirin idan aka amince da shi, rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

"Majalisa za ta amince da kudirin haraji kuma babu abin da zai faru," Sanata

6. Sanata Aminu Tambuwal

Tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya fito fili ya caccaki kudirin harajin da Shugaba Tinubu ya gabatar a gaban majalisa.

Tambuwal, Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu, ya bayyana cewa ba wannan lokacin ya dace a kawo wannan kudirin ba duba da masifar tsadar rayuwar da ake ciki.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnatin Tinubu ta maida hankali wajen kawo karshen matsin da ake ciki, kamar yadda Punch ta rahoto.

7. Gwamnonin Arewa 19

Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta yi fatali da kudirin tun farko, inda ta bayyana cewa sabon tsarin harajin zai yiwa jihohin Arewa illa.

Ta yi kira ga ƴan majalisar tarayya su yaki wannan kudiri domin zai ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahalar rayuwa.

Sai dai gwamnonin su 19 sun ce ba wai suna adawa da kudirin ne gaba ɗaya ba, suna bukatar a dawo a zauna a tattauna domin a gyara kura-kuran da ke ciki.

Kara karanta wannan

Zulum ya gargadi Tinubu, ya fadi abin da zai faru idan ya zartar da kudirin haraji

Sanatan Bayelsa ya goyi bayan Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Seriake Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce majalisa za ta amince da sabon kudirin haraji.

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ce ko sama da ƙasa za su haɗu sai sun zartar da dokar sauya fasalin haraji kamar yadda aka yi a dokar PIA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262