Gwamna Zulum Ya Faɗi Jihohi 2 da Za Su Amfana da Kudirin Harajin Bola Tinubu

Gwamna Zulum Ya Faɗi Jihohi 2 da Za Su Amfana da Kudirin Harajin Bola Tinubu

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya ce jihohin Legas da Ribas ne za su fi amfana da kudirin harajin Shugaba Bola Tinubu
  • Zulum ya bayyana cewa ƴan Arewa ne suka ba Tinubu sama da kaso 60% na kuri'unsa a zaɓen 2023, don haka ba za su juya masa baya ba
  • Gwamnan ya ce sun gano cewa abubuwan da ke kunshe a kudirin za su yi wa Arewa illa shiyasa suke bukatar shugaban ƙasa ya canza tunani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi zargin cewa jihohin Legas da Ribas ne kadai za su ci gajiyar kudirin gyaran harajin Bola Tinubu.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa sun yi bincike kan abubuwan da ke ƙunshe a cikin kudirorin sauya fasalin harajin kuma sun gano akwai kura-kurai.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya tuna da mutanen Tudun Biri shekara 1 bayan jefa bam a taron Maulidi

Gwamna Babagana Zulum.
Gwamna Zulum ya ce Legas da Ribas ne za su amfana da kudirin sake fasalin harajin Tinubu Hoto: @ProfZulum
Asali: Twitter

Babagana Zulum ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kudirin harajin Tinubu ya taɗa ƙura

Tun bayan gabatar da kudirorin gyaran haraji guda huɗu a gaban majalisar tarayya, manyan mutane da ƴan siyasa daga Arewa suka yi fatali da shi.

Gwamnonin Arewa, sarakuna da malamai sun ce kudirin zai yi masu illa idan har aka zartar da shi, inda suka buƙaci shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake nazari.

Sai dai duk da sukar kudirin da ake yi, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa yana nan kan bakarsa domin ya hango alherin da ke tattare da sabon tsarin.

Gwamna Zulum ya faɗi jihohin da za su amfana

Da yake ƙara fito da wasu abubuwa da ya fahimta dangane da kudirin, Gwamna Zulum ya ce jihohin Legas da Ribas ne kaɗai za su fi amfana da sabuwar dokar.

Kara karanta wannan

Zulum ya kaddamar da katafariyar tashar jirgin kasa ta farko a Arewa.

"Bisa bincike da nazarin da muka yi, mun gano cewa jihohin Legas da Ribas ne kaɗai za su amfana da tsarin sauya fasalin harajin. Mu abin zai fi yi wa illa," in ji Zulum.

Gwamnonin Arewa sun fara adawa da Tinubu?

Farfesa Zulum ya ƙara da cewa sabanin yadda wasu ke ta surutu, gwamnonin Arewa ba su adawa da gwamnatin Shugaba Tinubu, rahoton Daily Trust.

A cewarsa, Arewa ba za ta iya adawa da Tinubu ba domin sama da kashi 60 na kuri’unsa da ya samu a zaɓen 2023 sun fito ne daga yankin.

Dalilin gwamnonin Arewa na sukar kudirin haraji

Rahoto ya gabata cewa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da ƙudirin haraji.

Farfesa Zulum ya bayyana cewa gwamnonin na buƙatar lokaci domin yin shawarwa kan ƙudirin wanda ke gaban majalisar dattawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262