Jonathan Ya Ware Gwamna 1 a Najeriya, Ya Kira Shi 'Janar' a Siyasa, Ya Jero Dalilai

Jonathan Ya Ware Gwamna 1 a Najeriya, Ya Kira Shi 'Janar' a Siyasa, Ya Jero Dalilai

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya sha ruwan yabo daga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • Jonathan ya ce Gwamna Fubara ya jajirce wurin tabbatar da samun cigaba a jihar Rivers da yankin Neja Delta
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana Gwamna Fubara a matsayin 'Janar' inda ya ce ya yi gwagwarmaya sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Jonathan ya bayyana Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin 'Janar' a siyasa duba da gwagwarmayar da ya yi.

Goodluck Jonathan ya yabawa Gwamna a Najeriya
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yabawa jajircewar Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Goodluck Jonathan, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: UGC

Jonathan ya bukaci ba Fubara goyon baya

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin taron nadin sarautar gargajiya a yau Lahadi 1 ga watan Disambar 2024, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya bukaci yan jihar da su cigaba da ba Gwamna Fubara goyon baya saboda cigaban yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

'Za ku yabawa Tinubu nan gaba': Dan Majalisar Tarayya daga Arewa kan kudirin haraji

Ya ce babu wanda zai zama Janar ba tare da fafatawa a yake-yake ba inda ya yabawa Fubara kan jarumtarsa.

Jonathan ya yabawa jajircewar Gwamna Fubara

Har ila yau, Jonathan ya ce fafatawa da abokan gaba da sauran kalubale da zai fuskanta su ne za su sake gina shi a siyasa.

"Babu wanda zai zama Janar ba tare da fafatawa a yaki ba, duk kalubale da kake fuskanta suna gina ka ne saboda gobe."
"Ganin yadda kake da jajircewa da kuma goyon bayan al'umma, tabbas Ubangiji zai taimake ka."

- Goodluck Jonathan

Jonathan ya ce zaman lafiyar jihar Rivers yana da matukar tasiri ga cigaban yankin Neja Delta, cewar Punch.

Tsohon shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewa cigaban Neja Delta zai inganta tattalin arzikin Najeriya gaba daya.

Jonathan ya jero matsalolin Najeriya

Kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya koka kan rashin haɗin kan da ake fama da shi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Sanata Ali Ndume ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC

Goodluck Jonathan ya bayyana cewa idan har ba a shawo kan matsalar haɗin kan ba, ci gaba ba zai samu ba a Najeriya.

Jonathan ya nuna damuwa kan cewa har yanzu an kasa ɗaukar kai a matsayin ɗaya, bayan shekara sama da 100 da haɗewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.