Babbar Kotu Ta Tabbatar da Dakatar da Mataimakin Shugaban PDP Na Ƙasa
- Babbar kotun tarayya ta tabbatar da matakin da aka ɗauka kan mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa a gundumarsa
- Ƙotun mai zama a Abakaliki da ke jihar Ebonyi ta amince da dakatar da Ali Odefa daga matsayin mataimakin shugaban PDP
- Tun farko dai kwamitin zartaswa a gundumarsa ne ya sanar da dakatar da shi bisa zargin cin amana da yi wa jam'iyya zagon ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi - Babbar kotun tarayya mai zama a Abakaliki a Ebonyi, ta tabbatar da dakatar da Ali Odefa daga matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Kwamitin zartarwa na PDP a gundumar Oguduokwor da ke ƙaramar hukumar Onicha a Ebonyi ya dakatar da Odefa daga jam’iyyar ne a ranar 4 ga Oktoba, 2024.
Yadda aka dakatar da mataimakin shugaban PDP
Shugabannin PDP na gundunar sun ce sun dakatar da shi ne bisa zargin cin amana da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake mayar da martani, Mista Ali Odefa ya yi fatali da dakatarwar da aka masa a gundumarsa, inda ya ce ta saɓa doka.
Ya yi ikirarin cewa waɗanda suka dakatar da shi ba su ne asalin shugabannin jam'iyyar PDP a gundumarsa ba, rahoton The Cable.
Wannan ya sa aka shigar da ƙara gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abakaliki, babban birnin Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Kotu ta tabbatar da dakatar da Odefa
Da yake yake hukunci a shari's mai lamba FHC/AI/CS/182/2024 tsakanin Ovuta da Odefa, alkalin kotun Mai shari'a Hilary Oshomah ys tabbatar da dakatarwar.
Alkalin kotun ya umarci Odefa da ya daina bayyana kansa a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Ya ce matakin da shugabannin PDP na gundumarsa suka ɗauka na dakatar da shi bai saɓa doka ba.
Tsohon minista ya fice daga jam'iyyar PDP
A wani ruwayar, kun ji cewa jam'iyyar PDP a Najeriya ta rasa jigonta yayin da take fama da rikicin cikin gida wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka ya yi murabus daga jam'iyyar gaba daya domin sauya wani layi.
Asali: Legit.ng