PDP Ta Samu Koma Baya da Tsohon Minista Ya Watsar da Ita, Ya Jero Dalilansa
- Jam'iyyar PDP a Najeriya ta rasa jigonta yayin da take fama da rikicin cikin gida wanda ya ki ci kuma ya ki cinyewa
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka ya yi murabus daga jam'iyyar gaba daya domin sauya wani layi
- Osita ya tabbatar da haka ne a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024 inda ya mika takardar murabus dinsa a gundumarsa da ke Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan harkokin jiragen sama a Najeriya, Osita Chidoka ya watsar da jam'iyyar PDP mai adawa.
Osita ya tabbatar da cewa ya yi murabus daga jam'iyyar da ke adawa domin mayar da hankali kan wani bangare.
Musabbabin barin Osita jam'iyyar PDP
Tsohon ministan ya bayyana haka ne a yau Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024 yayin hira da gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osita ya ce ya tura takardar murabus dinsa daga jam'iyyar PDP a gundumarsa da ke jihar Anambra a hukumance.
Ya ce ya bar siyasa domin mayar da hankali kan kungiyar da ya kafa da ba ta gwamnati ba mai suna Athena.
Tsohon minista ya mika takardar murabus daga PDP
"A yau, na mika takardar yin murabus daga jam'iyyar PDP a gunduma ta da ke jihar Anambra."
"Na bar jam'iyyar PDP, zan janye daga siyasa na wani lokaci, zan mayar da hankali kan kungiya ta Athena."
"Zan yi aiki da wasu yan Najeriya da ke son kawo sauyi a ɓangaren siyasa saboda daga yau na bar jam'iyyar PDP."
- Osita Chidoka
PDP ta bukaci a sake zaɓen yan majalisar Rivers
A baya, kun ji cewa shugaban PDP na ƙasa ya shiga rigimar sauya sheƙar ƴan majalisar dokokin jihar Ribas na tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike.
Umar Damagum ya ributa takarda a hukumance zuwa INEC, ya bukaci ta shirya zaɓen cike gurbin ƴan majalisu 27 a jihar.
Damagum ya ce sauya sheƙar da suka yi watanni shida bayan rantsar da su ta saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng