APC Ta Dakatar da Yar Takarar Gwamna, Aishatu Binani? Jam'iyyar Ta Magantu
- An yi ta yada rade-radin cewa jam'iyyar APC ta dakatar da yar takarar gwamna a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya
- Jam'iyyar ta musanta labarin da ake yaɗawa kan dakatar da Sanata Aishatu Binani da ta yi takarar gwamna zaben 2023
- Sakataren yada labaran jam'iyyar, Mohammed Abdullahi ya ƙaryata labarin inda ya ce sharrin masu neman rigima ne a APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta yi martani kan jita-jitar dakatar da Sanata Aishatu Binani.
Jam'iyyar ta musanta labarin da ake yaɗawa inda ta ce babu kamshin gaskiya kan lamarin da ake ta magana.
APC ta ƙaryata batun dakatar da Binani daga jam'iyya
Sakataren yada labaran jam'iyyar, Mohammed Abdullahi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da The Nation ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi ya ce kwata-kwata babu maganar dakatar da 'yar takarar gwamnan APC a jihar da aka gudanar a zaben 2023.
Ya ce an yada labarin ne kawai domin kawo rigima da kuma neman ruguza kokarin Nuhu Ribadu da mataimakin shugaban APC ta kasa a Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu.
Mustapha Salihu ya bukaci kaddamar da bincike mai zurfi domin gano wadanda suka kulla makirci wurin yada wannan labari maras dadi, cewar Daily Post.
Shugaban APC ya magantu kan dakatar da Binani
Shugaban jam'iyyar APC a yankin Yola ta Kudu, Barista Idris Shuaibu ya ce Binani cikakkiyar mamban jam'iyyar ce har yanzu.
Sanarwar ta ce babu kamshin gaskiya kan cewa jam'iyyar a yankin Yola ta Kudu ta dakatar da Aishatu Binani inda ta ce har yanzu tana daga cikin masu ruwa da tsakin APC.
APC ta dakatar da tsohon gwamna
Kun ji cewa rikicin jam'iyyar APC mai ci ya sake sauya salo bayan dakatar da tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola.
Jam'iyyar reshen jihar ta ce tana zargin tsohon ministan da kawo rudani da farraka APC a Osun domin biyan bukatarsa.
Wannan na zuwa ne bayan mika takardar korafi kan tsohon gwamnan ga shugaban APC ta kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng