'Ka Jira Abin da Zai Faru': An Gargadi Hadimin Tinubu kan Cin Mutuncin Obasanjo
- Kusa a jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugabanta na kasa, Bode George ya ja kunnen hadimin Bola Tinubu
- Bode George ya gargadi hadimin a ɓangaren sadarwa, Bayo Onanuga kan cin mutuncin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo
- Jigon PDP ya ce abin takaici ne yadda Onanuga ya ci mutuncin dattijo kamar Obasanjo da ya kai matsayin mahaifinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jigon PDP, Bode George ya gargadi hadimin Bola Tinubu kan sukar Olusegun Obasanjo da ya yi.
Bode George ya ja kunnen Bayo Onanuga inda ya ce zai fuskanci gagarumar matsala a rayuwarsa kan taba Obasanjo.
Obasanjo: Bode George ya gargadi hadimin Tinubu
Jigon PDP ya bayyana haka yayin wani jira da jaridar TheCable ta bibiya inda ya ce babban laifi ne cin mutuncin manya a al'adar Yarbawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
George ya ce Onanuga sai ya girbi abin da ya shuka saboda cin mutuncin dattijo kamar Obasanjo.
Ya ce Obasanjo dattijo ne wanda ya kai matsayin mahaifin Onanuga saboda ya cancanci mutunci daga gare shi, cewar Daily Post.
Bode George ya yi Allah wadai da sukar dattawa
"Dattijo da ya kai matsayin mahaifinka ya yi magana, amma ka fito kana sukarsa ta ko ta ina."
"Haka ya ke yi, ni ma ya yi mani haka a baya, idan ka kwatanta shi da mu ka san yaro ne, mutane sun fadi ra'ayinsu, kana zaginsu."
"Ko da kana son ka yi martani ne, al'adar Yarbawa ba ta ba da damar cin mutunci irin haka ba, dole wata rana zai girbi abin da ya shuka."
- Bode George
Obasanjo ya soki tsarin mulkin Tinubu
A wani labarin, an ji tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki a mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Cif Olusegun Obasanjo ya ce lamura sun lalace, kasa ta rikice a cikin watannin da Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan karagar mulki Olusegun.
Obasanjo ya kira shugaba Bola Tinubu da sunan 'Baba go slow' saboda ikirarin cewa rayuwa ta gagara cigaba a mulkinsa da yake yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng