Dan Majalisar NNPP Ya Shiga Matsala bayan Ya Bar Tafiyar Kwankwasiyya
- 'Yan NNPP a majalisar wakilai sun buƙaci cire Hon. Ali Madakin Gini daga matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye
- Jam'iyyar NNPP ta ƙasa ta maye gurbinsa da Hon. Tijjani Jobe, mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a majalisar wakilai
- Ana ganin dai matakin ba zai rasa alaƙa da matakin ɗan majalisar na barin tafiyar Kwankwasiyya a NNPP ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ƴan majalisa 15 daga cikin 18 na jam'iyyar NNPP sun amince da sauke Hon. Ali Madakin Gini daga matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.
Ƴan majalisun sun sa hannu kan takardar goyon bayan tsige takwaransu mai wakiltar Dala a majalisar wakilai daga muƙamin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Ɗan majalisar NNPP zai iya rasa mukami
Jaridar Daily Nigerian ta ce daga cikin ƴan majalisar da suka sa hannu a takardar har da Alhassan Rurum (Rano/Kibiya/Bunkure da Abdullahi Sani (Ƙaraye/Rogo).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar NNPP ta zabi dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Ringado, Tijjani Jobe, a matsayin wanda zai maye gurbin Ali Madaki.
NNPP ta na so canza Ali Madakin Gini
Hakan na kunshe a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban NNPP da sakatare na ƙasa, Ajuji Ahmed da Dipo Olayoku da aka aika ga shugaban majalisar Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
"Mun turo wannan wasiƙa ne domin mika sunan ɗan jam'iyyarmu, Hon Tijjani Abdulƙadir Jobe ya maye gurbin Hon Aliyu Sani Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na."
Dalilin sauke ɗan majalisar NNPP daga muƙamin
Sai dai wasiƙar ba ta bayyana dalilin sauke Ali Madaki daga wannan matsayi tare da maye gurbinsa ba.
Amma dai bayanai sun nuna cewa hakan ba zai rasa nasaba da rigingimun cikin gida da suka dabaibaye NNPP reshen jihar Kano ba.
Ana ganin NNPP ta sauke Ali Madakin Gini daga matsayinsa a majalisa ne saboda ya bar tafiyar Kwankwasiyya da Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.
Jam'iyyar NNPP ta ƙara rasa jiga-jiganta
A wani rahoton, an ji cewa jam'iyyar NNPP ta sake gamuwa da matsala yayin da wasu 'yan takarar kansila suka sauya sheka zuwa APC a jihar Kano.
Karkashin jagorancin Jamilu Isyaku Getso, 'yan takarar sun sanar da komawarsu APC ne ta hannun Sanata Barau Jibrin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng