Mai Neman Takara a PDP Ya Fallasa Yadda Aka Rika Biyan $30, 000 a Saye Tikitin 2023

Mai Neman Takara a PDP Ya Fallasa Yadda Aka Rika Biyan $30, 000 a Saye Tikitin 2023

  • Tsohon mai neman takarar shugaban kasa, Dele Momodu ya bayyana makudan kudin da su ka biya kowane wakilin jam'iyya
  • Ya ce yayin neman tikitin takarar PDP, sun bayar da akalla $30,000 ga kowanne daga cikin wakilan jam'iyya 774 na kasar nan
  • Mista Dele Momodo ya kara da bayyana cewa akwai wasu daga cikin masu son takarar PDP da su ka bayar da sama da $30,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Mawallafin mujallar Ovation kuma tsohon dan takarar a PDP, Dele Momodu ya fallasa yadda su ka rika ba wakilan jam’iyya Daloli gabanin zaben cikin gida a 2022.

Mista Momodu ya shaida cewa an ba kowane wakilin jam’iyya $30,000 a yunkurin saye ra’ayinsu kan zabar dan takarar da zai wakilci PDP.

Kara karanta wannan

'Najeriya ta gyaru a lokacin ku': Tambawul, PDP sun aika sakonni ga Atiku

Takara
Dele Momodu ya fadi nawa aka biya wakilai lokacin neman takarar shugaban kasa Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mawallafin ya yi da na sani kan neman tsayawa takarar shugaban kasar duba da irin makudan miliyoyin Naira da aka batar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda PDP ta wawashe kudin yan takara

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tsohon mai neman takarar shugaban Najeriya a PDP, Dele Momodu ya ce sun sayi fam a kan Naira miliyan 50.

Ya ce wannan da kudin da aka rika bayarwa ga wakilan jam’iyya sun nuna yadda aka mayar da harkar neman takara ta kudi zalla.

Mista Momodu ya ce;

“Akwai wadanda su ka biya sama da $30,000 ga kowane wakili daga cikin mutum 774, ta yaya za ka yi takara da su?
Sun jima da sace kudin kasa kuma su na sabgogi iri-iri domin su samu kudi, musamannan wadanda su ka fito daga yankin da ke da albarkatun fetur.”

‘Zan daina neman takara’ - Dan PDP

Dele Momodu ya ce ba zai sake neman takarar a zabe shi a kowane irin mukami ba, sai dai an cimma matsaya.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu Zai Iya Ganin Adawar da Bai Taba Gani ba a Siyasa, Ana Shirin Kifar da Shi

Tsohon dan takarar ya ce;

“Sai dai ko wata babbar jam’iyya za ta amince ta dauke ni a matsayin dan takararta ba tare da na nemi tsayawa takara ba.”

Yan PDP sun barke da zanga zanga

A baya kun ji cewa rikicin shugabanci a PDP ta yi kamari, yayin da kusoshi a jam'iyyar reshen Kuros Ribas su ka tsunduma zanga zanga domin nuna fushinsu kan halin da ake ciki.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar sun mamaye sakatariyarsu ranar Litinin domin nuna adawa da yunkurin dawo da tsohon shugabansu da aka tsige, Venatius Ikem.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.