Jiga Jigan PDP Sun Barke da Zanga Zanga a Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Barazana

Jiga Jigan PDP Sun Barke da Zanga Zanga a Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Barazana

  • Mambobin PDP daga faɗin jihar Kuros Riba sun fita zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024
  • Masu zanga-zangar sun yi barazanar tatara kayansu su bar PDP matukar aka dawo da shugaban jam'iyyar, Venatius Ikem da aka tsige
  • Sun roki uwar jam'iyya ta ƙasa ta amince da tsige Ikem daga matsayin shugaban PDP na Kuros Ribas domin jam'iyya ta farfaɗo da kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Zanga-zanga ta ɓarke a sakatariyar PDP ta jihar Kuros Riba kan taƙaddamar shugabancin jam'iyyar.

Wasu gungun ƴaƴan PDP sun mamaye sakatariyar da safiyar yau Litinin, 25 ga watan Nuwamba, domin nuna adawa da yunkurin maido shugaban jam'iyyar da aka tsige.

Masu zanga-zanga.
Zanga-zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP ta Cross River Hoto: @NigeriaStories
Asali: Twitter

Menene ya haddasa zanga-zangar 'yan PDP?

Vanguard ta tattaro cewa tun farko kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP reshen Kuros Riba ya sauke shugaban jam'iyyar, Venatius Ikem.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya ba PDP sirrin kayar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai jam'iyyar PDP ta ƙasa ta yi fatali da matakin, ta ce NWC na jiha ba shi da ikon dakatar da shugaban jam'iyya ba tare da amincewarta ba.

An ruwaito cewa ƴaƴan PDP na gundumomi da ƙananan hukumomi a jihar Kuros Riba ne suka fito zanga-zanga don nuna fushinsu kan yuƙurin dawo da Mista Ikem.

Masu zanga-zanga sun yi barazanar barin PDP

Masu zanga-zangar sun ɗaga kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kuma sun yi barazanar ficewa daga jam'iyyar idan aka maido da Venatius Ikem.

Wasu daga cikin saƙonnin da ke rubuce a jikin kwalayen da masu zanga-zangar suka ɗaga sun haɗa da, "Dole Ikem ya tafi," "PDP ba ta bukatar Vena," "Matakin NWC na Kuros Riba shi ne mafi alheri."

Jagoran masu zanga-zangar kuma shugaban jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Kalaba, Mr Bassey Asuquo, ya ce tsige Ikem shi ne mafi alheri.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso shugaban PDP na ƙasa da NWC a gaba kan Taron NEC

'Yan zanga-zanga sun turawa PDP sako

Ya ce ƴaƴan PDP ba su bukatar Mista Venatius Ikem a matsayin shugaban jam'iyya na jihar Kuros Riba, Daily Post ta ruwaito.

Asuguo ya ce:

“Mu jagororin jam'iyya a fadin jihar nan muna goyon bayan tsige shugaban PDP na Kuros Riba, muna son NWC na ƙasa ya bari a cire Ikem, idan har ba a kore shi ba mu za mu bar masa jam'iyyar."

Taron NEC: Gwamnonin PDP sun ba NWC wata 3

A wani rahoton, an ji cewa gwamnonin PDP sun ba shugabannin jam'iyyar na ƙasa watanni uku su shirya taron kwamitin zartarwa watau NEC.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa bayan taron da suka yi a Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262