Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Magana, Kwanaki 10 da Sauka An Fara Bincikensa

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Magana, Kwanaki 10 da Sauka An Fara Bincikensa

  • Tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya fadi dalilin da aka ganinsa, shi ne zai sa gwamnati mai ci ta fara binciken ayyukansa
  • Hadimin tsohon gwamnan kan harkokin yada labarai, Cruosoe Osagie ya bayyana cewa akwai alamun gwamnatin ba ta shirya ba mulki ba
  • Ya bayyana cewa kokarin fara binciken gwamnatin Obaseki zai bata lokaci da albarkatun Edo, saboda haka ya ke ganin bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Tsohon gwamnan tsohon gwamna Godwin Obaseki a Edo ya yi martani kan ikirarin sabuwar gwamnatin jihar karkashin Monday Okpebholo na fara bincikensa.

Mashawarcin tsohon gwamnan kan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie ya bayyana mamakin yadda sabuwar gwamnatin ta kafa kwamitin mutane 14 don tantance kadarorin gwamnati.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya fadi shugabannin da suka fi gwamnoni kwarewa a karbar rashawa

Taswira
Za a fara binciken tsohon gwamnan Edo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

AIT Televsion ta ce kwamitin zai kuma binciki mulkin Obaseki domin tabbatar da sahihancin ayyukan da aka aiwatar a lokacin da ya ke gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Godwin Obaseki ya yi martani ga gwamnan Edo

Jaridar The Nation ta wallafa cewa tsohon gwamnan Edo, Mista Godwin Obaseki ya caccaki kokarin da gwamna Monday Okpebholo na fara binciken yadda ya gaudanar da mulki.

Hadimin tsohon gwamnan kan harkokin yada labari, Crusoe Osagie ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin boye gazawar gwamnati mai gabanin fara aiki.

Obaseki ya shawarci gwamnan Edo

Don haka, Osagie ya shawarci Gwamna Okpebholo da ya mayar da hankali kan gudanar da mulki da inganta rayuwar mutanen Jihar Edo.

Ya kara da cewa hakan zai fi zama alheri a maimakon bata lokaci da albarkatun jihar a kan abubuwan da ba su da amfani kamar binciken gwamnatinsa.

Ganduje ya nemawa tsohon gwamnan Edo alfarma

A baya mun ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo kan gudanar da ayyukan gina kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rushe sababbin masarautu da tsohon gwamna ya samar, ya daga kimar Sarki

Ya bayyana cewa akwai bukatar ya mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar mutanensa a maimakon binciken gwamnatin tsohon gwamna, Godwin Obaseki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.