An zo Wurin: Gwamna Ya Gaza Hakuri, Ya Kafa Kwamitin Binciken Tsohon Gwamnan Jiharsa
- Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kafa kwamitin fara binciken tsohuwar gwamnatin jihar da ta sauka
- Okpebholo ya kafa kwamitin ne mai dauke da mutane 14 domin binciken tsohon Gwamna, Godwin Obaseki
- Wannan na zuwa ne kwanaki 12 bayan an rantsar da Okpebholo a matsayin gwamnan jihar bayan nasara a zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Kasa da makwanni biyu bayan darewa karagar mulki, Gwamna Monday Okpebholo ya kafa kwamitin bincike.
Gwamna Okpebholo na jihar Edo ya kafa kwamitin ne domin binciken tsohon Gwamna, Godwin Obaseki.
Gwamna Okpebholo zai bincike Obaseki a Edo
Sakataren yada labaran gwamnan, Fred Itua shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar da Leadership ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Itua ya ce Gwamna Okpebholo ya kafa kwamitin ne mai dauke da mutane 14 domin binciken badakalar tsohuwar gwamnatin.
Ya ce wannan mataki ya zama dole duba da shirin gwamnan wurin daura jihar kan turbar cigaba, cewar Punch.
Gwamna Okpebholo zai kaddamar da kwamitin a ranar 26 ga watan Nuwambar 2024 a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Benin City.
Edo: Jerin mambobin kwamitin da aka kafa
Mambobin kwamitin sun hada da Dr. Ernest Afolabi Umakhihe a matsayin shugaba da Anslem Ojezua a matsayin mataimakinsa.
Sauran mambobin sun hada da Prince Kassim Afegbua da Hon. Patrick Ikhariale da Mr. Taiwo Akerele da Hon. Patrick Idiake da Hon. Rasaq Bello-Osagie.
Sai kuma Mr. Fredrick Unopah da Frank Osumuede Edebor Esq a matsayin sakatare da Mrs. Abdallah Eugenia da Hon. Patrick Obahiagbon da Kenny Okojie da Lyndsey Tes-Sorae da Hon. Abass Braimoh.
Okpebholo ya zargi Obaseki ya kwashe motoci 200
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kafa kwamiti na musamman domin kwato wasu motoci 200 da suka bace a jihar.
Gwamna Okpebholo na zargin tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki da mukarrabansa da kwashe motocin gwamnati.
Daga bisani, an fitar da wata sanarwa da ke nuna an samu motocin guda uku daya tana cike da kayan tallafin abinci domin jama'a.
Asali: Legit.ng