Gwamnonin PDP sun Shiga Ganawa a Jos, Sun Jero Tsare Tsaren Kawo Sauyi a Kasa
- Yayin da suke kokarin kawo sauyi kan yadda jam'iyyar ke tafiya, gwamnonin PDP suna ganawa ta musamman a jihar Plateau
- Gwamnonin sun taru ne domin nemo hanyoyin kawo hadin kai da zaman lafiya a jam'iyyar tare da dawo da martabarta
- Gwamna Caleb Mutfwang wanda shi ne mai masaukin baki ya ce sun himmatu domin kawo sauyi a shugabancin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP sun shiga ganawa kan wasu matsaloli a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya.
Gwamnonin karkashin PDP suna ganawar domin shawo kan matsalolin jam'iyyar da kuma cigaban ƙasa.
PDP ta yi alkawarin kawo sauyi a kasa
Mai masaukin baki, Gwamna Caleb Mutfwang ya tabbatar da himmatuwarsu wurin kawo hadin kai a jam'iyyar, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutfwang ya kuma ba da tabbacin dawo da martabar jam'iyyar a idon yan Najeriya kamar yadda take a baya.
Gwamnan ya nuna farin cikinsa da yadda gwamnonin PDP da kuma masu ruwa da tsakin jam'iyyar suka cika a jihar domin wannan taro.
Gwamna Mutfwang ya godewa gwamnonin PDP
"Duk da wannan taro musamman an shirya ne domin gwamnoni, amma abin farin ciki ne yadda jiga-jigan jam'iyyar suka cika wannan taro domin ba gwamnonin goyon baya."
"Jam'iyyar PDP ba iya zakulo hanyoyin kawo zaman lafiya a cikinta za ta yi ba har da dawo da martabar jam'iyyar a idon yan Najeriya."
Caleb Mutfwang
Daga bisani, Gwamna Mutfwang ya bayyana tasirin Plateau a bunkasa jam'iyyar tun farkon kafa ta inda ya jihar gidan PDP ce, cewar Punch.
Gwamnonin Najeriya sun gana a Abuja
A baya, kun ji cewa kwana daya bayan Shugaba Bola Tinubu ya turawa shugabannin Arewa sako, kungiyar gwamnonin Najeriya ta shiga ganawar gaggawa.
Gwamnonin ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara za su tattauna matsaloli da dama da suka shafi Najeriya.
Daga cikin abubuwan da ake sa ran za su tattauna akwai asusun rarar danyen mai (ECA) da harajin man fetur da sauran abubuwa muhimmai.
Asali: Legit.ng