Jam'iyyar PDP Ta Sake Ɗage Taron NEC saboda Mutuwar Matar Gwamna a Najeriya
- Jam'iyyar PDP ta sake ɗage taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC wanda ta tsara gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024
- Sakataren PDP na ƙasa, Samuel Anyanwu ya ce kwamitin gudanarwa NWC ya yanke ɗaga taron ne saboda jana'izar matar gwamnan Akwa Ibom
- Anyanwu ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a sanar da ranar taron karo na 99 a tarihin jam'iyyar PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jam’iyyar PDP ta sake dage taron kwamitin zartarwa ta kasa watau NEC saboda jana'izar matar gwamnan jihar Akwa Ibom.
A ranar Alhamis ta mako mai zuwa, 28 ga watan Nuwanba, 202, PDP ta tsara gudanar da taron NEC, sai dai a yanzu ta sake ɗaga taron zuwa gaba.
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ɗage taron NEC na jam'iyyar PDP
Anyanwu ya ce an dage taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 99 ne saboda jana’izar Patience Umo Eno, uwargidan gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno.
Sakataren PDP ya ce za a sanar da ranar taron nan gaba kadan. Wannan shi ne karo na biyu da jam'iyyar ta ɗage taron NEC.
Idan ba ku manta ba PDP ta fara sanya ranar 24 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranar taron NEC, amma ta ɗaga zuwa 28 ga watan Nuwamba.
A sanarwar da ya fitar, Sanuel Anyanwu ya ce ranar taron ta ci ƙaro da jana'izar matar gwamnan jihar Akwa Ibom.
PDP na alhinin mutuwar matar Gwamna Eno
Anyanwu ya ce:
"A taron kwamitin gudanarwa da ya gudana ranar 20 ga watan Nuwamba, an ja hankalin PDP cewa taron NEC ƙaro na 99 ya ci karo da jana'izar matar gwamnan Akwa Ibom, Patience Umo Eno."
"Bayan tattaunawa kwamitin NWC ya fahimci akwai bukatar shugabannin PDP su tama Gwamna Eno alhirin wannan rashin kuma su halarci jana'iza.
"Bisa haka muna sanar da ƴan kwamitin NEC cewa an ɗage taron da za a yi ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024 zuwa gaba, za a sanar da ranar nan ba da jimawa ba."
PDP ta musanta dakatar da shugabanta
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta kasa ya yi fatali da yunkurin dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Kuros Riba.
Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya ce a tanadin kundin tsarin mulki, kwamitin gudanarwa na jiha ba shi hurumin dakatar da shugaba.
Asali: Legit.ng