Tana Tsaka da Shirye Shiryen Zabe, Jam'iyyar APC Ta Gamu da Babbar Matsala a Ribas

Tana Tsaka da Shirye Shiryen Zabe, Jam'iyyar APC Ta Gamu da Babbar Matsala a Ribas

  • Jam'iyyar APC ta gamu da cikas yayin da ta ke shiryen shiryen gudanar da zabukan shugabanninta a jihar Ribas
  • Babbar kotun jiha da ke Fatakwal ta dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da zabukan da suka fara ranar 16 ga Nuwamba
  • Tsakin jam'iyyar APC da ke karkashin Tony Okocha bai mayar da martani kan hukuncin da kotun ya yanke ba tukunna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Wata babbar kotun jiha da ke birnin Fatakwal ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da zabuka a Ribas.

Umarnin, wanda aka bayar ranar 19 ga Nuwamba, 2024, ya dakatar da kwamitin ayyuka na APC daga cigaba da zabukan da suka fara ranar 16 ga watan nan.

Kotu ta yi hukunci kan taron da jam'iyyar APC ke shirin gudanarwa a jihar Ribas
Kotu ta dakatar da APC daga gudanar da zabukan shugabanni a Ribas. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kotu ta hana APC gudanar da zabe

Kara karanta wannan

2027: LP ta sha damara, ta samu dabarar korar Tinubu daga shugabancin Najeriya

The Guardian ta rahoto cewa kotu na bayar da umarnin wucin gadi ne domin dakatar da kowane bangare daga daukar mataki har sai an kammala shari'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa yayin da bangaren APC mai biyayya ga Nyesom Wike ya yi rashin nasara a shari'ar da ya shigar gaban kotun daukaka kan zabukan kananan hukumomin Ribas.

Wasu 'yan APC sun koka kan cewa ba a ba su fom din shiga zabe ba duk da cewa sun biya, lamarin da ya sa suka shigar da kara.

Masu karar, Okwudili Ndike, Peace Oganu, da Samuel Uchegbule sun shigar da karar ne mai lamba PHC/3859/CS/2024 inda suka nemi a soke zaben.

APC bangaren Okacha ta yi gum

Jaridar BusinessDay ta rahoto cewa babu wani tabbaci ko APC za ta bi wannan umarnin, domin an saba yin watsi da irin wannan umarni na dakatar da zabukan jam'iyya.

A baya bayan nan kotu ta dakatar da PDP daga gudanar da zabukan jam'iyyar a Ribas amma aka yi fatali da umarnin, inda shugabannin da aka zaba ke gudanar da aikinsu yanzu haka.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

Kwamitin ayyukan APC a jihar Ribas da ke karkashin Tony Okocha bai mayar da martani kan wannan hukuncin kotun ba tukunna.

Ribas: Kotu ta tsige shugaban APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta ta soke matakin tsige zaɓaɓɓun shugabannin APC na jihar Ribas karkashin jagorancin Emeka Beke.

Kotun ta yanke hukuncin cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya tafka kuskure da ya rusa zaɓaɓɓun shugabanni na jihar Ribas karkashin Emeka haka kurum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.