Kaduna: Sanata Ya Nada Hadimai a Bangaren Addinin Musulunci da Kiristanci
- A kokarin wanzar da zaman lafiya a jihar Kaduna, Sanata ya nada hadimai kan bangarorin addinai guda biyu
- Sanata Sunday Katung ya nada Malam Ilyasu Musa da Fasto Gideon Mutum domin kula da bangaren addinan Musulunci da Kiristanci
- Rahotanni sun tabbatar da cewa dukan mutanen biyu da aka naɗa sun yi kaurin suna wurin tabbatar da zaman lafiya a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sanata a jihar Kaduna ya nada hadimai na musamman a bangaren addinin Musulunci da Kiristanci.
Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Kudu, Sunday Katung ya nada Malam Ilyasu Musa da Fasto Gideon Mutum.
Sanata ya nada hadimai a Musulunci, Kiristanci
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Hon Wilson Yangye ya fitar a shafin Facebook a yau Alhamis 21 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Katung ya nada Ilyasu ne a bangaren addinin Musulunci yayin da Fasto Mutum zai kula da bangaren Kiristoci.
Sanata Katung ya dauki matakin ne domin kara kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a mazabarsa.
Gudunmawar da sababbin hadiman suka bayar
"Malam Ilyasa yana daga cikin hukumar zaman lafiya a jihar Kaduna kuma shi ne sakataren Jama'atu Nasril Islam (JNI) a Kaduna ta Kudu."
"Yana kan gaba wurin fadakarwa kan zaman lafiya tare da wayar da kan al'umma kan gujewa tashe-tashen hankula."
- Hon Wilson Yangye
Har ila yau, Gideon Mutum yana ba da gudunmawa wurin tabbatar da zaman lafiya a yankin gaba daya.
Faston Mutum shi ne ya assasa kungiyoyin zaman lafiya na Amaya Peace Foundation (APF) da WeShape Nations Institute (WENI).
Musulmi ya ba coci kyautar wurin ibada
Kun ji cewa wani Musulmi a jihar Oyo ya yi abin a yaba da ya ba cocin St John kyautar makeken dakin taro domin cigaba da ayyukansu.
Musulmin mai suna Ahmed Raji ya ce ya ba da kyautar saboda yadda cocin bai nuna wariya ga sauran addinai da ke yankin Iseyin a Oyo.
Alhaji Raji ya bayyana himmatuwarsa wurin tabbatar da ba da goyon baya da kuma gudunmawa ga cocin a kowane lokaci.
Asali: Legit.ng