An Yi 'Ƙarar' Ganduje wajen Tinubu kan Kalaman 'Tayar da Hankali'
- Kalaman shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje kan karɓar mulki a wasu jihohin Kudu maso Yamma na cigaba da tayar da kura
- Jam'iyyar PDP a Kudu maso Yammacin Najeriya ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban APC ya yi bayan zaben Ondo
- Sakataren yada labaran PDP ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan ya ja kunnen Ganduje bisa kalaman da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan samun nasara a zaben Ondo, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce za su kwato jihohin Osun da Oyo daga hannun PDP.
Maganar da Abdullahi Ganduje ya yi ta fusata jam'iyyar PDP inda ta yi martani na musamman a ranar Alhamis.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sakataren yada labaran PDP a Kudu maso Yamma, Sanya Atofarati ne ya yi martani ga Ganduje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta kai karar Ganduje wajen Tinubu
Jam'iyyar PDP a Kudu maso Yammacin Najeriya ta ce maganar Ganduje ta kwace jihohin Osun da Oyo za su tayar da hankali.
Sakataren yada labaran PDP, Sanya Atofarati ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya gargaɗi Ganduje saboda kaucewa jawo fitina.
Sanya Atofarati ya yi magana ne bayan PDP ta kammala taron kwana uku a birnin Ibadan na jihar Oyo.
"Muna kira ga Bola Tinubu ya gargadi Abdullahi Ganduje kan kokarin yin maguɗin zaɓe a Oyo da Osun.
Kuma muna jaddada cewa Ganduje bashi da hurumin yin magana a kan adalci ko dimokuraɗiyya."
- Sanya Atofarati
Jami'yyar PDP ta yi Allah wadai kan yadda hukumar INEC ta gudanar da zabe a jihar Ondo inda ta ce ba adalci a lamarin.
Haka zalika PDP ta bukaci sufeton yan sanda ya yi bincike kan zargin wasu jami'ai da aka yi da rashin adalci yayin zaben.
'Ka sauya tsare tsare' ACF ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta yi magana kan tsadar rayuwa da yan Najeriya ke cigaba da kuka a kai tun zuwan Bola Tinubu.
Shugabannin kungiyar sun bukaci Bola Tinubu ya gaggauta sauya tsare tsaren da ya kawo domin ceto rayuwar miliyoyin yan Najeriya.
Asali: Legit.ng