An Bukaci Yan Arewa Su yi Watsi da Kwankwaso kan Taɓa Tinubu
- Wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, NAT ta yi martani ga Sanata Rabi'u Kwankwaso kan sukar kudirin haraji
- NAT ta yi kira ga yan Arewa da su yi watsi da maganganun da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na sukar sauya fasalin harajin Najeriya
- A karon farko, madugun Kwankwasiyya ya soki kudirin harajin Bola Tinubu ne a wani taron yaye ɗalibai a jami'ar Skyline ta jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An fara yi wa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso raddi kan sukar kudirin haraji na shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wata kungiyar magoya bayan Bola Tinubu ta ce Kwankwaso bai kyauta ba da ya soki kudirin harajin a gaban dalibai.
Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta ce kamata ya yi Kwankwaso ya yi wa daliban bayanin mai kyau a kan dokar harajin maimakon suka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAT: 'Kwankwaso bai fahimci kudirin haraji ba'
Wata kungiya mai rajin goyon bayan shugaba Bola Tinubu ta yi martani kan maganganun Sanata Rabi'u Kwankwaso a kan kudirin haraji.
Kungiyar NAT ta ce akwai alamar madugun Kwankwasiyya bai fahimci kudirin harajin ba ko kuma yana son siyasantar da shi.
A cewar NAT, kamata ya yi Kwankwaso ya mayar da hankali kan cigaban ƙasa maimakon yin maganganu da za su kawo rabuwar kai.
"Bola Tinubu ya kawo kudirin haraji ne domin tabbatar da cigaba a Najeriya, ciki har da jihohin Arewa.
Abin takaici ne yadda Kwankwaso ya tsaya a gaban ɗalibai yana ce musu Tinubu na son ruguza tattalin Arewa.
Muna kira ga al'ummar Arewa da su yi watsi da maganganun Kwankwaso na sukar sauya fasalin haraji."
- Ƙungiyar NAT
Tribune ta wallafa cewa NAT ta ce sauya fasalin haraji abu ne mai muhimmanci da zai haɓaka tattalin kasa kuma ya kamata a goyi bayansa.
A karshe, yan kungiyar sun ce kamata ya yi a yabawa Bola Tinubu kan sauya fasalin haraji maimakon caccakarsa.
ACF ta bukaci Tinubu ya sauya salo
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya salon tafiya.
Shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ya ce ya kamata gwamnati ta sauya tsare tsaren da suke talauta al'umma.
Asali: Legit.ng