Damagum: Dalilin da Ya Sa Ciyamomin Jihohi 36 Suka Gana da Shugaban PDP na Ƙasa

Damagum: Dalilin da Ya Sa Ciyamomin Jihohi 36 Suka Gana da Shugaban PDP na Ƙasa

  • Umar Damagum ya bayyana cewa ya gana da shugabannin PDP na jihohi 36 ne domin tattaunawa kan muhimman batutuwa da fahimtar juna
  • Muƙaddashin shugaban PDP na kasa ya ce taron ba shi da alaƙa da rikicin cikin gida ko neman kamun kafa gabanin taron NEC
  • A ranar Laraba ne Damagum ya jagoranci NWC suka gana da ciyamomin PDP na jihohi 36 a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Taron muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP da ciyamomin jihohi 36 ya ja hankali musamman saboda matsowar taron majalisar zartaswa NEC.

A jiya Laraba, shugaban PDP, Umar Damagum da ƴan kwamitin gudanarwa NWC suka gana da shugabannin jam'iyyar na jihohin Najeriya a Abuja.

Umar Damagum.
Damagum ya bayyana dalilin ganawarsa da shugabannin PDP na jihohi Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Damagum na son ci gaba da jagorancin PDP

Tribune ta ruwaito cewa wannan taro na zuwa ne a lokacin da aka fara raɗe-raɗin cewa Damagum ya fara kamun kafa wajen ƴan majalisar NEC don tsira da kujerarsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu saboda mutuwar Sanata, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damagum dai na fuskantar matsin lamba daga wasu ƙusoshin PDP kan ya sauka daga shugabancin PDP, ya ba Arewa ta Tsakiya damar cike gurbin.

Da yake jawabi kan dalilin ganawa da ciyamomin PDP na jihohi, Damagum ya ce sun sgirya taron ne domin kara danƙon haɗin kai a tsakaninsu.

Ya bayyana cewa taron da suka yi a sakatariyar PDP ta ƙasa ba sabo ba ne, dama suna yi akai-kai domin tattaunawa da kuma fahimtar juna.

Dalilin ganawar Damagum da ciyamomin PDP

A cewarsa, a wannan karon ya maida hankali kan batun tarukan shiyyoyi da ke tafe da kuma batun haɗa kan ƴaƴan PDP a kowane mataki.

Ambasada Damagum ya karyata rade-radin da ake cewa ba ya ga maciji da shugabannin PDP na jihohi

A rahoton The Nation, Damagum ya ce:

"Wannan ba sabon taro ba ne, mun yi makamancinsa a baya, manufar zaman shi ne mu tattauna da shugabanni na jihohi musamman sababbi, mu san juna.

Kara karanta wannan

"Tinubu ne babbar matsalarmu," Tsohon ɗan takarar gwamna ya soki shugaban ƙasa

"Sannan mu tattauna kan harkokin gudanarwa da tarukan zaɓen shugabannin shiyyoyi da ke tafe, babu wani abu bayan haka."

Damagum ya caccaki matakin cire tallafi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban jam’iyyar PDP ya bayyana cewa, akwai ganganci wajen janye tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi baktatan.

Damagum ya ce ba zai yiwu dan takarar PDP na shugaban kasa ya janye tallafi haka siddan ba tare da duba ga wasu lamurra ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262