PDP Ta Sauke Shugaban Jam'iyya Ana Shirin Taron NEC? Gaskiya Ta Bayyana
- Kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta kasa ya yi fatali da yunkurin dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Kuros Riba
- Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya ce a tanadin kundin tsarin mulki, kwamitin gudanarwa na jiha ba shi hurumin dakatar da shugaba
- Ya bukaci masu ruwa da tsaki, ƴaƴan PDP da magoya baya su yi watsi da takardar saboda ta saɓawa tanadin doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta yi watsi da yunƙurin dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Kuros Riba, Venatius Ikem.
Wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 15 ga watan Nuwamba da sa hannun dukkan ƴan kwamitin gudanarwa na jihar ta yi ikirarin tsige Mista Ikem.
Punch ta tattaro cewa bayan bayyanar takardar, shugaban PDP na Kuros Riba ya ce sauke shi daga muƙamin zai yi wa jam'iyyar illa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta dakatar da shugabanta na Kuros Riba?
Sai dai jam'iyyar PDP ta ƙasa ta soke dakatarwar, inda ta bayyana matakin a matsayin mara amfani kuma haram a tsarin dokar jam'iyya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP, Debo Ologunagba ya fitar ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024.
Rikicin PDP: Dakatarwar ta saɓa doka
Sanarwar ta ce:
"An jawo hankalin kwamitin gudanarwa na PDP ta kasa (NWC) kan zargin dakatar da shugaban jam'iyyar reshen jihar Kuros Riba, Venatius Ikem.
"NWC ya ayyana dakatarwar a matsayin mara tasiri ba ta da amfani kuma an soke ta kamar yadda kundin tsarin mulki da dokar PDP suka tanada.
"Domin share shakku, ya kamata jama'a su sani kwamitin gudanarwa na jiha ba shi da hurumin dakatar da shugaban jam'iyya na jiha ba tare da sahalewar NWC ba."
PDP ta tabbatar da shugabancin Ikem a Kuros Riba
Ologunagba ya jaddada cewa Venatius Ikem na nan daram a matsayin shugaban PDP na jihar Kuros Ribas, kamar yadda Guardian ta tattaro.
Ya kuma yi kira ga shugabanni, masu ruwa da tsaki, mambobi da magoya bayan PDP su yi fatali da batun sauke shugaban jam'iyyar domin ba gaskiya ba ne.
Rikicin PDP: Damagum ya samu goyon baya
Kun ji cewa Umar Damagum ya kara samun goyon bayan ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam'iyyar PDP ta ƙasa.
Shugabannin PDP na jihohi 36 sun jaddada goyon bayansu ga Damagum a wani taro da suka yi a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja
Asali: Legit.ng