Zaben Ondo: Daga Karshe PDP Ta Bayyana Matsayarta kan Nasarar APC

Zaben Ondo: Daga Karshe PDP Ta Bayyana Matsayarta kan Nasarar APC

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Ondo ta bayyana cewa ba ta gamsu da sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar ba
  • PDP ta ce za ta garzaya kotu domin ƙalubalantar nasarar da Lucky Aiyedatiwa ya samu a zaɓen na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ɗaukar matakin shari'a shi ne kaɗai zaɓin da take da shi wajen ganin an sauya maguɗin da aka yi a zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Jam'iyyar PDP ta sha alwashin ƙalubalantar nasarar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu a gaban kotu.

PDP za ta je kotu a Ondo
PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa, Agboola Ajayi
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ayo Fadaka mai ba ɗan takarar gwamnan PDP, Agboola Ajayi, shawara na musamman ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: INEC ta mika takardar shaidar lashe zabe ga Aiyedatiwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene matsayar PDP kan zaɓen Ondo?

Jam’iyyar mai adawa a jihar Ondo ta ce ɗaukar matakin shari’a kan sakamakon zaɓen shi ne zaɓi ɗaya tilo da ta ke da shi wajen ganin an kawar da maguɗin da aka tafka a zaɓen.

Ayo Fadaka ya bayyana cewa jam'iyyar ta yi shiru ne inda ta ci gaba da bincike kan laifuffukan da INEC da APC suka yi tun bayan kammala kaɗa ƙuri'a a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

"A taƙaice, mun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen da aka gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, kuma za mu dauki matakin shari’a domin ganin an sauya maguɗin da aka yi.
"Wannan shi ne zaɓin da muke da shi kuma muna fatan Allah zai sanya mu samu adalci."

- Ayo Fadaka

Tinubu ya magantu kan zaɓen Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi magana bayan sanar da sakamakon zaben jihar Ondo a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024.

Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben da aka gudanar a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng