Shugaban NNPP Ya Taso Ganduje a Gaba bayan Ya Cika Baki kan Zaben Ondo
- Kalaman da Abdullahi Umar Ganduje ya yi na APC na shirin ƙwace jihohin Osun da Oyo a zaɓe mai zuwa ba su yi wa shugaban NNPP daɗi ba
- Shugaban NNPP na jihar Osun ya ja kunnen Abdullahi Umar Ganduje da ya guji yin kalaman da za su tada fitina a yankin Kudu maso Yamma
- Tosin Odeyemi ya buƙaci tsohon gwamnan na Kano cewa ka da abin da ya faru a Ondo ya ruɗe shi, domin babu mai hankalin da zai zaɓi APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya ja kunnen shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban na NNPP ya gargaɗi Abdullahi Umar Ganduje, da ya guji tada zaune tsaye a yankin Kudu maso Yamma, kan kalamnan da ya yi kwanan nan.
Tosin Odeyemi ya yi wannan gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje, yayin wata ziyara da ya kai birnin Akure na jihar Ondo, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta lashe jihohin Oyo da Osun a zaɓe mai zuwa.
Shugaban jam'iyyar NNPP ya caccaki Ganduje
Tosin Odeyemi ya soki kalaman na Ganduje, inda ya bayyana su a matsayin abin da bai dace ya fito daga bakin dattijo kamarsa ba, duba da irin halin ƙuncin da ƴan Najeriya ke ciki yanzu a ƙarƙashin gwamnatin APC.
A cewar Odeyemi, jam'iyyar APC ba za ta yi nasara ba a jihar Ondo, idan da an yi sahihin zaɓe na gaskiya, ba ta riƙa siyan ƙuri'u ba, rahoton Daily Post ya tabbatar.
"Ya kamata a ce Ganduje yana kalaman da suka dace da matsayin shi. Duba da halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki wane mai hankali ne zai zaɓi APC? Ka da Ganduje ya bari abin da ya faru a jihar Ondo ya ruɗe shi."
"Mutanen Osun wayayyu ne masu son zaman lafiya. Dole ne kowace jam'iyya ta bar mutane su zaɓi abin da suke so. Ka da Ganduje ya maida yankin Kudu maso Yamma filin yaƙi."
- Tosin Odeyemi
Shugaban na NNPP ya kuma ƙalubalanci Ganduje da ya tabbatar da farin jinin APC ta hanyar yin takara a jiharsa, inda a baya NNPP ta doke jam’iyyar da gagarumin rinjaye.
Ƴan NNPP sun koma APC a jihar Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan takarar kujerar kansila daga ƙaramar hukumar Gwarzo, jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasa.
Sanata Barau Ibarahim Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ya sanar da ficewar 'yan takarar kansilar daga NNPP zuwa APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng