Kwamacala: Sabon Shugaban Karamar Hukuma Ya Nada Hadimi kan Doya da Barkono

Kwamacala: Sabon Shugaban Karamar Hukuma Ya Nada Hadimi kan Doya da Barkono

  • Shugaban karamar hukumar Igbo Etiti a jihar Enugu ya ba mutane mamaki kan wasu nade-nade guda biyu na hadimansa
  • Hon. Eric Odo ya ba wasu hadimansa guda biyu na musamman masu kula da bangaren doya da yalo da kuma barkono
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin shugaban karamar hukumar ta fitar inda ta shawarci wadanda aka ba muƙaman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Wani shugaban karamar hukuma a jihar Enugu ya girgiza jama'a kan nadin wasu hadimai guda biyu.

Shugaban karamar hukumar Igbo Etiti, Eric Odo ya nada hadimai guda biyu kan sha'anin doya da barkono da kuma yalo.

Ciyamoman a karamar hukumar ya nada hadiminsa a bangaren doya da barkono
Shugaban karamar hukuma a Enugu ya nada hadimai a bangaren doya da barkono. Hoto: Hon. Eric Odo, UK Afrifoods.
Asali: UGC

Ciyaman ya nada hadimai 2 a Enugu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar tun ranar 1 ga watan Nuwambar 2024, cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Haraji: Bayan barazanar gwamnoni, majalisa ta yi magana kan buƙatar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Eric Odo ya amince da nadin Ezeugwu Ogbonna hadimi a bangaren noma musamman doya da kuma barkono.

Shugaban karamar hukumar ya shawarci wadanda aka naɗa mukaman da su yi aiki tukuru domin ciyar da Igbo Etiti, Daily Post ta ruwaito.

"Ina mai sanar da kai cewa shugaban karamar hukumar Igbo Etiti ya nada ka hadimi kan noma (doya da barkono)."
"Ya kamata ka ziyarci shugaban karamar hukumar Igbo Etiti da ke Ogbede domin karasa sauran abubuwa da fara aiki."
"Yana da muhimmanci ka sani wannan ba aikin gwamnati ba ne, nadin mukamin siyasa ne na wucin-gadi karkashin shugaban karamar hukumar Igbo Etiti."

- Cewar sanarwar da aka turawa Ogbonna

An nada hadimi a bangaren yalo, barkono

Har ila yau, shugaban karamar hukumar ya kuma amince da ba Nwodo Ugonna muƙamin hadimi na musamman a bangaren yalo da kuma barkono a karamar hukumar Igbo Etiti.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto Odo bai bayyana ainihin abin da ake bukatar hadiman guda biyu su yi ba.

Kara karanta wannan

'Ku wuce kotu': Tinubu ya magantu bayan zaben Ondo, ya ba jam'iyyun adawa shawara

Yan bindiga sun harbe dan takarar PDP

A baya, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani dan takarar karamar hukuma a jihar Enugu da ke Kudancin kasar, Hon. Ejike Ugwueze.

Marigayin ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyar Neke Odenigbo da ke karamar hukumar Enugu ta Gabas a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.