Surutun Bwala Ya Jawo Masa, An Fayyace Matsayin Hadimin a Gwamnatin Tinubu

Surutun Bwala Ya Jawo Masa, An Fayyace Matsayin Hadimin a Gwamnatin Tinubu

  • Kwanaki kadan bayan nada Daniel Bwala a mukamin hadimin Bola Tinubu, an fayyace masa matsayinsa sabanin yadda yake nufi
  • Hadimi bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya ci gyaran Bwala bayan ayyana kansa a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa
  • Onanuga ya ce an yi wasu sauye-sauye kan mukaman masu magana da yawun shugaban kasa inda ya ce sun kai mutum uku yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Da alamu an fara samun baraka a fadar shugaban kasa tsakanin hadiman Bola Tinubu a bangaren sadarwa.

Hakan ya biyo bayan nada Daniel Bwala a matsayin hadimin Mai girma Bola Tinubu na musamman da ke neman hada fada.

An fadawa Bwala matsayinsa a gwamnatin Tinubu bayan ya yi katobara
Fadar shugaban kasa ta ce an yi sauye-sauye kan mukamin hadiman Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Bwala Daniel.
Asali: Twitter

Danuel Bwala ya fadi matsayinsa a fadar shugaban kasa

Hadimin Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya sanar da yin garambawul kan mukaman inda ya fayyace komai a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Durotaye: An gano tsohon hadimin Tinubu da ya yi aikin wata 6 ba tare da albashi ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan yana da nasaba da rubutu da Bwala ya yi a shafinsa na X inda ya ke cewa ya fara aiki a hukumance a matsayin hadimin Bola Tinubu.

"Yau, na fara aiki a hukumance a matsayin hadimi kuma mai magana da yawun Tinubu a fadar shugaban kasa."

- Daniel Bwala

Hadimin Tinubu ya ci gyaran Daniel Bwala

Sai dai Bayo Onanuga ya fayyace lamarin inda ya ce babu wani mai magana da yawun Tinubu guda daya, ya ce su uku ne.

Har ila yau, Onanuga ya bayyana cewa an yi wasu yan sauye-sauye a mukaman hadiman da ke fadar shugaban kasa sadarwa.

"Shugaba Bola Tinubu ya yi yan sauye-sauye kan mukaman hadimai gudan biyu da aka nada yan kwanakin nan saboda gudanar da aiki yadda ya kamata."
"Daga ciki akwai Sunday Dare da ke rike da mukamin hadimin Tinubu a bangaren hulda da jama'a da wayar da kan al'umma yanzu ya koma hadimi na musamman a kan sadarwa da hulda da jama'a."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi martani mai zafi ga Obasanjo, ta tono 'kurakuransa'

"Mr. Daniel Bwala da aka ba mukamin hadimi a bangaren sadarwa da hulda da jama'a yanzu ya koma hadimi a bangaren sadarwa da tsare-tsare."

- Bayo Onanuga

Tinubu ya ba Bwala mukami a gwamnatinsa

A baya, kun ji cewa bayan dogon jira, Daniel Bwala ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu a ranar Alhamis 14 ga watan Nuwambar 2024.

Shugaba Tinubu ya amince da nadin Bwala a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa da hulda da jama'a.

Wannan na zuwa ne bayan shafe watanni Bwala na yabon gwamnatin Tinubu, bayan ya yi watsi da Atiku Abubakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.