Jami'an DSS Sun Kama Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Inuwar PDP, Bayanai Sun Fito

Jami'an DSS Sun Kama Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Inuwar PDP, Bayanai Sun Fito

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa hukumar DSS ta kama tsohon ɗan takararta na gwamna a zaben jihar Ogun, Ladi Adebutu
  • Mai magana da yawun PDP na Ogun, Kayode Adebayo ya ce DSS ta kama Adebutu ne yayin da ya amsa gayyatarsu ranar Litinin
  • Ya ce an yi yunkurin karbo shi beli amma hakan ba ta samu ba, zuwa washe gari lauyoyinsa za su karɓi ragamar kes din

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta cafke ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP a zaben 2023, Ladi Adebutu.

Sakataren yada labarai na PDP a jihar Ogun, Kayode Adebayo, ya tabbatar da kama Adebutu tare da tsare shi a wata sanarwa da ya saki a Abeokuta ranar Litinin.

Kara karanta wannan

PDP ta firgita da hukumar DSS ta ƙi faɗin dalilin cafke ƙusa a jam'iyya

Ladi Adebutu.
PDP ta zargi DS da kama Ladi Adebutu a jihar Ogun Hoto: @adiadebutu
Asali: Twitter

Dalilin DSS na kama ɗan takarar PDP

An ruwaito cewa DSS ta gayyaci Adebutu ne domin amsa tambayoyi bisa zarginsa da tada hargitsi a zaben kananan hukumomin da aka yi, kamar yadda Channels ta kawo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro cewa an gudanar da zaɓen kananan hukumom a jihar Ogun a ranar Asabar da ta gabata, 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Kakakin PDP na jihar Ogun, Kayode Adebayo ya ce har yanzun ba su san dalilin tsare Adebutu a ofishin hukumar DSS ba.

Jam'iyyar PDP ta zargi DSS da kama jigonta

A sanarwar da ya fitar, Adebayo ya ce:

"Muna sanar da ɗaukacin ƴaƴan jam'iyyarmu mai albarka PDP cewa hukumar DSS ta cafke jagoranmu kan wasu zarge-zarge da ba a bayyana ba har yanzu.
"Duk da haka ya bukaci magoya baya, ƴan jam'iyya da masu fatan alheri da su kwantar da hankulansu, komai zai wuce."

Kara karanta wannan

Zaɓen Ondo: Jerin manyan waɗanda suka yi nasara da waɗanda tafka asara

"Duk wani yunkuri na karɓo belinsa ya ci tura har zuwa karfe 10:00 na daren yau Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024. Gobe da safe lauyoyin za su karɓi kes din."

DSS ta shiga tsakanin NLC da TCN

A wani rahoton, an ji cewa jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta fara kokarin sasanta rikicin da ya shiga tsakanin kungiyar kwadago da kamfanin rarraba wuta.

NLC na zargin kamfanin rarraba hasken lantarki da ke Ikeja da take hakkin ma'aikatansa duk da an zauna tare da cimma matsaya a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262