2027: Gwamnoni Sun Yi Barazanar Takara ga Yan Majalisa kan Kudirin Harajin Tinubu
- Sabani tsakanin gwamnoni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kudirin haraji na kara girma yayin da aka fara barazana ga yan majalisa
- Jami'in yada labaran majalisar dokokin Najeriya ya bayyana cewa yan majalisa sun fara fuskantar barazana daga gwamnonin jihohi
- Tun a karon farko dai gwamnonin Arewa suka yi fatali da kudirin gyaran harajin amma shugaba Bola Tinubu ya noƙe kan tabbatar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana cigaba da takaddama kan kudirin haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya aika majalisa.
Rahotanni na nuni da cewa gwamnoni sun fito da hanyar da za su yaki kudirin a majalisun Najeriya.
Punch ta wallafa cewa mataimakin mai magana da yawun majalisar dokoki, Hon. Philip Agbese ya ce suna fuskantar barazana daga gwamnoni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnoni na barazana ga yan majalisa
The Sun ta wallafa cewa sakamako dagewa da shugaba Bola Tinubu ya yi kan gabatar da kudirin haraji ga majalisa, gwamnoni sun fito da wata barazana.
Mataimakin mai magana da yawun majalisa, Philip Agbese ya ce an fara barazanar hana takara ga duk wanda ya amince da kudirin.
Tun a ranar 3 ga Satumban 2024 ne shugaban kasa ya tura kudirin gyara dokokin haraji ga majalisar ƙasa.
"Gwamnoni sun fara barazanar hana tikitin takara a 2027 ga duk wanda ya amince da kudirin haraji na Bola Tinubu.
Sai dai matukar muna majalisa, ba abin da zai hana mu goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ceto tattalin Najeriya.
Dukkan yan jam'iyyu mun hada kai domin ganin Najeriya ta cigaba, kuma wannan shi ne fatan shugaban majalisa."
- Philip Agbese
Ana sa ran cewa a yau Litinin yan majalisar za su yi zama kan kudirin harajin kafin dawowa aiki a ranar Talata.
Gwamnoni sun yi magana kan haraji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya sake magana kan kudirin haraji da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakaninsu da Bola Tinubu.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnonin Arewa ba su yin adawa da sauya fasalin haraji a Najeriya kawai suna bukatar a yi gyara ne.
Asali: Legit.ng