Bayan Lashe Zabe, Buhari Ya Faɗi Abin da Ya ke so Gwamnan Ondo Ya yi

Bayan Lashe Zabe, Buhari Ya Faɗi Abin da Ya ke so Gwamnan Ondo Ya yi

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar a Ondo
  • Muhammadu Buhari ya fadi wasu abubuwa da ya ke so gwamna Lucky Aiyedatiwa ya mayar da hankali a kai bayan kayar da yan takara
  • Buhari ya ce zaben ya kara tabbatar da karfi da karɓuwar da dimokuraɗiyya ke da shi a kasar nan, ya kuma yabawa jami'an tsaro da na INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana bayan APC ta lashe zaben Ondo.

Muhammadu Buhari ya yi kira ga gwamna Lucky Aiyedatiwa kan yin ayyukan da za su kawo saukin rayuwa ga al'umma.

Buhari
Buhari ya ba gwamnan Ondo shawara. Hoto: Ebenezer Adeniyan|Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Tsohon shugaban kasar ya taya APC murnar lashe zaben Ondo a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.

Kara karanta wannan

'Ku wuce kotu': Tinubu ya magantu bayan zaben Ondo, ya ba jam'iyyun adawa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Buhari ke so gwamnan Ondo ya yi?

Shugaba Buhari ya taya gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben gwamnan Ondo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

The Cable ta wallafa cewa Muhammadu Buhari ya buƙaci gwamnan ya samar da tsare tsaren da za su habaka jihar da samar da ayyukan yi ga matasan Ondo.

Haka zalika Buhari ya bukaci kawo tsare tsaren da za su rage hauhawar farashi da kawo walwala da sauƙin rayuwa ga al'umma.

Mutane sun aminta da APC inji Buhari

Shugaba Buhari ya ce zaben APC da aka yi a jihar Ondo alama ce da ke nuna cewa har yanzu mutane suna tare da jam'iyyar da gwamna Aiyedatiwa.

Buhari ya kara da cewa sakamakon zaben ya nuna irin yadda dimokuraɗiyya ta kafu a Najeriya kuma kawar da ita zai yi wahala matuka.

Zaɓen Ondo: Buhari ya yabawa INEC

Muhammadu Buhari ya yabawa hukumar INEC da jami'an tsaro kan kokarin da suka yi na ganin an rage samun kurakurai yayin zaben.

Kara karanta wannan

'Mun gode Tinubu': Ganduje ya taya Aiyedatiwa murna, ya fadi jihohi 2 da za su kwace

A karshe, shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya sa gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kammala wa'adinsa lami lafiya.

'An saye kuri'a a zaben Ondo' - Yiaga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Yiaga Africa da ta saka ido a zaben Ondo ta fara fitar da rahoto kan yadda wasu abubuwa suka faru yayin da ake kada kuri'a.

Yiaga ta yi zargin cewa manyan jam'iyyun APC da PDP sun saye kuri'u a wurare daban daban yayin da ake zaben a ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng