Zamfara: Tsohon Kwamishina Ya Tsallake da Aka Sanar da Zaben Kananan Hukumomi
- Shugaban hukumar zaben jihar Zamfara, Bala Aliyu ya sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar
- Bala Aliyu ya sanar da cewar jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ita ta yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar
- Hukumar ZASIEC ta ce PDP ta lashe dukan kananan hukumomi 14 da kuma kujerun kansiloli a fadin jihar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Hukumar zaben jihar Zamfara (ZASIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi.
Hukumar ya tabbatar da jam'iyyar PDP mai mulkin jihar da lashe zaben a kananan hukumomi 14.
Zamfara: PDP ta lashe zaben kananan hukumomi
Channels TV ta ruwaito cewa bayan nasara a kanana hukumomi 14, PDP ta kuma lashe dukan kujerun kansiloli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar a jihar, Bala Aliyu shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024.
Bala Aliyu ya bayyana zaben da mai inganci wanda aka yi shi cikin lumana ba tare da samun matsaloli ba.
Tsohon kwamishina ya lashe zabe a Zamfara
Shugaban hukumar ya bayyana nasarar da aka samu da cewa tana da nasaba da hadin kai tsakanin jami'an tsaro da na INEC da kuma al'umma.
Tsohon kwamishinan kudi, Mannir Mu'azu Haidara daga jam'iyyar PDP ya lashe zaben karamar hukumar Kaura Namoda da aka gudanar da kuri'u 71,000, cewar Daily Post.
Rahotanni sun tabbatar da cewa APC mai adawa a jihar da ba ta fafata a zaɓen ba abin mamaki ta samu kuri'u da dama a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Zamfara: Al'umma sun kauracewa zaben kananan hukumomi
Kun ji cewa zaben kananan hukumomi a jihar Zamfara ya ci karo da matsala saboda rashin fitowa da al'umma suka yi.
Hukumar zaben jihar (ZASIEC) ta shirya zaben ne a kananan hukumomi 14 da na kansiloli a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Sai dai al'umma da dama sun ki fitowa zaben inda suka cigaba da lamuransu na yau da kullum musamman a birnin Gusau.
Asali: Legit.ng