Yiaga: Yadda Aka Saye Kuri'un Talakawa da Kudi Kaɗan a Zaben Ondo
- Kungiyar Yiaga Africa da ta saka ido a zaben Ondo ta fara fitar da rahoto kan yadda wasu abubuwa suka faru yayin da ake kada kuri'a
- Yiaga ta yi zargin cewa manyan jam'iyyun APC da PDP sun saye kuri'u a wurare daban daban yayin da ake zaben a ranar Asabar
- Kungiyar ta yi kira na musamman kan yadda za a kawo gyara a harkar zabe a Najeriya musamman wajen sayen kuri'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Masu saka ido kan zaben Ondo sun fara fitar da rahoto kan wasu abubuwa da suka faru a ranar Asabar.
Kungiyar Yiaga Africa ta yi Allah wadai da yadda aka rika sayen kuri'un talakawa da kudi dan kadan a zaben Ondo.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugabannin Yiaga Africa ne suka fitar da rahoton a birnin Akure na jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka saye kuri'u a zaben Ondo
Kungiyar Yiaga Africa ta ce an samu da dama daga cikin masu zabe a jihar Ondo da suka sayar da kuri'unsu.
Yiaga ta ce dukkan manyan jam'iyyun PDP da APC sun ruɗi masu zaben da kudi daga N5,000 ya yi sama.
Rahoton kungiyar ya yi zargin cewa ba a samu turjiya daga wasu jami'an tsaro da suke wuraren da ake sayen kuri'un ba.
"Wasu masu zaɓe a karamar hukumar Ifedore sun tabbatar da cewa sun sayar da kuri'unsu ga yan APC.
An kalli yan APC da PDP suna rige rigen sayen kuri'a a kan N5,000 zuwa 10,000 a mazabar da ke Elegiri/Ediro.
Duk da sayen kuri'u da aka yi a bayyane, jami'an tsaro da suka wajen ba su yi katabus ba wajen hana masu aikata laifin."
- Rahoto Yiaga Africa
Kungiyar Yiaga Africa ta yi yabo ga jami'an DSS da suka cafke wani mai sayen kuri'a a mazabar St. Stephen da ke Akure.
The Cable ta wallafa cewa Yiaga ta ce yan takara da jam'iyyunsu ne manyan masu laifi kan karya dokokin zabe da aka yi a jihar Ondo.
PDP ta zargi APC a zaɓen Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta zargi APC da sayen kuri'a a wata mazaba yayin da ake zaben Ondo.
PDP ta yi kira ga hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) domin daukar mataki kan zargin da ta yi.
Asali: Legit.ng