Ogun: Jam'iyyun Adawa Na So a Sake Zabe, APC Ta Lashe Kujerun Ciyamomi 20

Ogun: Jam'iyyun Adawa Na So a Sake Zabe, APC Ta Lashe Kujerun Ciyamomi 20

  • Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkanin kananan hukumomi 20 da mazabu 236 a zaɓen ciyamomin jihar Ogun
  • Shugaban hukumar zaben jihar (OGSIEC), Babatunde Osibodu, ya ce kuri’u 613,156 aka kada a zaɓen, kuma APC ce ta yi nasara
  • Jam’iyyun adawa, musamman sLabour, sun soki zaɓen, suna zargin rashin gaskiya da jinkirin isar kayan zaɓe a rumfuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Jam'iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 20 a zaben kananan hukumomin jihar Ogun da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zaɓen Ogun (OGSIEC), Babatunde Osibodu, ya bayyana sakamakon zaɓen a hedikwatar hukumar da ke Oke-Ilewo, Abeokuta.

Jam'iyyar APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 20 na jihar Ogun
'Yan adawa sun nemi a sake zabe yayin da APC ta lashe zaben ciyamomi a Ogun. HotoL @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Babatunde Osibodu ya ce jam'iyyar APC ta samu nasara a dukkanin mazabu 236 da ke faɗin jihar kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Abin da APC da PDP suka samu a kananan hukumomi 15

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar zaben ya kara da cewa an kada jimillar kuri’u 613,156 a zaɓen kananan hukumomi 20 da na kansilolin jihar.

Hukumar zaben ta ce jam'iyyun siyasa 19 ne suka shiga cikin zaben inda APC, PDP, LP, ZLP, SDP da kuma APGA suka fi taka rawar gani.

Jam'iyyun adawa sun soki sakamakon

Rahoton Channels TV ya nuna cewa jam’iyyun adawa sun soki zaɓen, suna masu bayyana cewa ba a gudanar da shi cikin adalci ba.

A taron manema labarai, shugaban jam’iyyar Labour (LP) na jihar Ogun, Biodun Jagun, ya bukaci a soke zaɓen gaba ɗaya.

Jagun ya ce ba ga ko kyallin jami’an hukumar OGSIEC a fiye da kaso 90 na rumfunan zaɓe ba, kuma an jinkirta kai kayan zaɓe a wasu rumfunan.

Ondo: APC ta lashe kananan hukumomi 15

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta lashe kananan hukumomi 15 yayin da INEC ke tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo.

Hukumar INEC ta tafi hutu inda da karfe 12 na rana za a sanar da sakamakon sauran kananan hukumomi uku da suka rage da kuma fadin wanda ya lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.