Tsadar Rayuwa: Bayan T Pain, Obasanjo ya Raɗawa Tinubu Sabon Suna

Tsadar Rayuwa: Bayan T Pain, Obasanjo ya Raɗawa Tinubu Sabon Suna

  • Tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki a mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Cif Olusegun Obasanjo ya ce lamura sun lalace, kasa ta rikice a cikin watannin da Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan karagar mulki
  • Olusegun Obasanjo ya kira Bola Tinubu da sunan 'Baba go slow' saboda ikirarin cewa rayuwa ta gagara cigaba a mulkinsa
  • Legit ta tattauna da wani matashi dan jam'iyyar APC, Aminu Hassan domin jin ra'ayinsa a kan maganar da Obasanjo ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya dura kan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Olusegun Obasanjo ya ce gazawar Bola Tinubu a bayyane take ta inda kowa zai iya gani a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bukaci Tinubu ya kori shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya ba da dalili

Obasanjo
Obasanjo ya kira Tinubu da sabon suna. Hoto: Bayo Onanuga|Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hadimin Obasanjo, Kehinde Akinyemi ne ya yi magana a madadinsa a wani taro a Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunan da Obasanjo ya raɗawa Tinubu

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kira Bola Tinubu da 'Baba go slow' a wani taro a Amurka.

Punch ta wallafa cewa Olusegun Obasanjo ya ce yanayin lalacewar lamura a Najeriya a bayyane yake ta inda duk wani mai gaskiya da tsoron Allah zai tabbatar.

Tsohon shugaban kasar ya koka kan yadda cin hanci da rashawa ke kara zama daram a fadin Najeriya.

"Kamar yadda duniya take gani, abubuwa ba su tafiya daidai a fadin Najeriya.
Duk inda cin hanci da rashin tarbiyya suka karu a kasa, dole a samu rashin tsaro, rashin hadin kai, rikici da rashin cigaba.
Wannan kuma shi ne halin da Najeriya ke ciki a karkashin mulkin Emilokan da Baba go slow."

- Olusegun Obasanjo

Olusegun Obasanjo ya fadi babbar matsalar Najeriya

Kara karanta wannan

A karshe, shugaba Tinubu ya sakawa tsohon hadimin Atiku da mukami a gwamnatinsa

Olusegun Obasanjo ya ce babbar matsalar Najeriya ita ce rashin shugabanci na gari ta inda shugabanni ba su sauke nauyin da aka daura musu.

Duk da haka Olusegun Obasanjo ya ce bai kamata yan Najeriya su cire tsammanin samun sauki da gyaruwan lamura a gaba ba.

Legit ta tattauna da Aminu Hassan

Wani matashi dan jam'iyyar APC a jihar Gombe, Aminu Hassan ya zantawa Legit cewa yana gani kamar akwai siyasa a cikin zancen Obasanjo.

Aminu ya ce wasu matsalolin Najeriya tun kafin APC ta fara mulki ake fama da su amma yanzu sai a rika jingina su ga Bola Tinubu kawai.

Obasanjo ya je auren yar Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya halarci daurin auren yar Kwankwaso a Kano.

Olusegun Obasanjo ya ziyarci jihar Kano a wata shiga mai ban mamaki ta inda ya sanya jar hula da ke nuna alamar tafiyar Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng