Ondo 2024: Yadda Ake Cakewa Mutane Kuɗin Kuri'u a Kusa da Jami'an EFCC

Ondo 2024: Yadda Ake Cakewa Mutane Kuɗin Kuri'u a Kusa da Jami'an EFCC

  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da cin karensu babu babbaka wajen sayen kuri'u a zaben gwamnan da ke gudana a jihar Ondo yau Asabar
  • Rahotanni sun nuna yadda wakilan ƴan siyasa ke sayen kuri'u a kusa da jami'an EFCC a wasu rumfunan zaɓe da ke yankin ƙaranar hukumar Akure
  • Babu wani mataki da jami'an hukumar yaki da rashawa watau EFCC suka ɗauka ko kama masu aikata laifin sayen kuri'u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Jam'iyyun siyasa sun ci gaba da sayen kuri'u a bainr jama'a a wasu rumfunan zaɓe duk da jami'an hukumar EFCC na wurin suna sanya iso.

Bayanan da muka samu sun yi nuni da cewa wakilan jam'iyyu na kasuwancin kuri'u ƙiri-ƙiri a yankin ƙaramar hukumar Akure.

Sayen kuri'u.
Cinin kuri'u na ci gaba da cin kasuwa a zaben gwamnan jihar Ondo Hoto: Edo Election
Asali: Facebook

Yadda ake sayen kuri'u a zaben Ondo

Kara karanta wannan

'Mun kama yan APC na sayen kuri'u a zaben Ondo,' PDP ta jefa zargi

Jaridar Punch ta gano yadda ake sayen kuri'u ido na ganin ido a rumfa ta 03 da ke gunduma ta 2, Eruoba da rumfar zaɓe ta 17, Egbedi Ward 11.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukka waɗannan rumfunan zaben guda biyu na yankin Kasuwar Arakale a karamar hukumar Akure a Ondo.

A gundumar Eruoba, kana kaɗa kuri'a za a biya ka kuɗinka sai ɗai har yanzu ba a bayyana farashin da ake sayen kowace ƙuri'a ba.

Amma a Owode Imuagun, mutane na rubuta sunayensu ne bayan kaɗa kuri'a sannan a tura su wani gini da ke kusa da wurin su karɓi kudinsu.

Ondo: Jami'an EFCC ba su ɗauki mataki ba

Duk da wannan abin da ke faruwa, jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC suna kewayen wurin amma ba su ɗauki wani mataki ba.

Jami'an hukumar EFCC na kan titin Arakale a kusa da rumfunan zaɓen da ake sayen kuri'u amma babu wani mataki da suka ɗauka ko kama wani.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyun siyasa sun ɓullo da sabuwar dabarar sayen kuri'un mutane

Ondo 2024: An kama masu sayen kuri'u

A wani rahoton, kun ji cewa wani bidiyo da ke yawo ya nuna lokacin da jami'an DSS suka cafke wani da ake zargin mai sayen kuri'u ne a zaben Ondo.

Rahoto ya nuna cewa an cafke mutumin ne a gunduma ta 4, rumfar zabe ta 007, da ke wajen makarantar St. Stephen, Akure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262