'Abin da Zai Faru Idan Na Fadi Zaben Gwamnan Ondo,' Dan Takarar SDP Ya Magantu

'Abin da Zai Faru Idan Na Fadi Zaben Gwamnan Ondo,' Dan Takarar SDP Ya Magantu

  • Dan takarar gwamnan jihar Ondo karkashin jam'iyyar SDP, Otunba Bamidele Akingboye ya ce yana da yakinin samun nasara
  • Otunba Akingboye ya ce yana da burin lashe zaben jihar domin tsamo al'ummarsa daga yunwa da kuma kangin talauci
  • Sai dai dan takarar ya ce zai amince da sakamakon zaben ko da kuwa ba shi ne ya yi nasara ba idan INEC ta cika wani sharadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Otunba Bamidele Akingboye, dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP ya kada kuri'arsa yayin da hukumar INEC ta fara gudanar da zaben jihar Ondo.

Bayan kada kuri'ar, Otunba Akingboye ya ce ya na da yakinin cewa za a gudanar da sahihin zaben gwamnan Ondo da ke gudana yanzu haka.

Dan takarar SDP ya yi magana bayan kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Ondo
Dan takarar SDP ya fadi abin da INEC za ta yi domin ya amince da shan kaye a zaben Ondo. Hoto: @OBA4OndoGov2024
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Akingboye ya bayyana haka ne bayan ya kada kuri’arsa da misalin karfe 9:00 na safe a rumfa ta 10, gunduma ta 2, Okitipupa, jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 6 kan masu kada kuri'a a zaben Ondo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar SDP zai dauki kaddara

Don haka ya bukaci hukumar INEC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe da su tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihar.

Akingboye ya tabbatar da cewa idan har aka gudanar da sahihin zabe, zai amince da sakamakon zaben ko da ace ba shi ne ya samu nasara ba.

Dan takarar gwamnan na SDP ya ce:

"Ina da yakinin cewa ni ne zan lashe zabe domin tsamo al'ummata daga yunwa da talauci. Wannan ya sa na yi aiki tukuru har na samu tikitin takara a SDP."

Ondo: Dan takarar SDP ya yabawa INEC

Dan takarar ya kuma jinjinawa INEC kan yadda take gudanar da zaben da kuma yadda ta kawo nau'urar tantance masu kada kuri'a ta BVAS.

Ya kuma yawaba jami'an tsaro kan irin matakan tsaron da suka sanya a dukkanin rumfunan zabe wanda zai kare jami'an INEC da masu kada kuri'a.

Akingboye ya kuma jinjinawa al'ummar jihar kan fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin yin zabe, inda ya ce yana da yakinin mutane masu yawa za su fito zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.