Zaben Gwamnan Ondo: Dalilan da Za Su Iya Sanya PDP Ta Lallasa APC a Ranar Asabar

Zaben Gwamnan Ondo: Dalilan da Za Su Iya Sanya PDP Ta Lallasa APC a Ranar Asabar

  • Akwai babbar dama ga jam’iyyar PDP na lashe zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba
  • Agboola Ajayi, dan takarar PDP a zaben, yana da alaka mai karfi da ’yan jihar, wanda hakan na iya silar da zai samu rinjayen kuri'u
  • Duk da rikicin PDP na kasa, an samu hadin kan shugabannin jam’iyyar a zaben jihar na Ondo, wanda hakan zai taimakawa Agboola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Jam’iyyar PDP na da babbar damar lashe zaben gwamnan Ondo. Za a gudanar da zaben jihar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, kamar yadda INEC ta tsara.

Hankalu yanzu sun karkata ga zaben gwamnan jihar na Ondo, inda za a fafata tsakanin APC da PDP da kuma wasu jam'iyyu kamar SDP, Labour da sauransu.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Dalilin da ya sa APC za ta iya lashe zaben gwamna na ranar Asabar

Ana hasashen jam'iyyar PDP za ta lashe zaben gwamnan jihar Ondo
Dalilan da ka iya sa PDP ta lashe zaben gwamnan jihar Ondo. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Kwarewa da kwarjinin dan takarar PDP

Rahoton Legit.ng ya nuna cewa dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Agboola Ajayi, yana da kwarjini da kwarewar mulki inda ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwarewarsa a harkokin mulki da siyasa da kuma kasancewarsa tsohon shugaban kwamitin majalisar dokokin Neja Delta (NDDC) na iya sa ya samu nasarar zaben da ke gudana.

PDP ta kuduri aniyar lashe zaben Ondo

Bugu da kari, jam'iyyar PDP ta yi alkawarin yin duk mai yiwuwa domin samun nasara a zaɓen, wanda ke nuni da jajircewarsu da yunƙurinsu na karbe mulki daga hannun APC.

Rikicin jam’iyyar na kasa bayan zabukan 2023 ba zai yi wani gagarumin tasiri a zaben Ondo ba, domin sau da yawa zaman lafiyar jam'iyya a cikin gida ya fi taka rawa a zaben gwamna.

Duk da rikicin PDP na kasa, gwamnonin jam’iyyar sun hada kai tare da goyawa Agboola baya domin tabbatar da cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC ya sha kaye a zaben.

Kara karanta wannan

'Yadda jam'iyyun siyasa ke yaudarar mutane da fetur da sauran abubuwa a zaben Ondo'

Ondo: 'Yan takarar da za su iya lashe zabe

Tun da fari, mun ruwaito cewa zaɓen Ondo na 2024 na dauke da manyan 'yan takara hudu: Lucky Aiyedatiwa, Ajayi Agboola, Otunba Akingboye da Sola Ebiseni.

Kowane dan takara na da burin inganta Ondo, ta fuskar tattalin arziki, ababen more rayuwa, lafiya, da rage cin hanci kuma daya daga cikinsu ne ake sa ran zai samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.