'Yadda Jam'iyyun Siyasa Ke Yaudarar Mutane da Fetur da Sauran Abubuwa a Zaben Ondo'

'Yadda Jam'iyyun Siyasa Ke Yaudarar Mutane da Fetur da Sauran Abubuwa a Zaben Ondo'

  • Wata kungiyar addini ta bayyana damuwa kan shirin siyan kuri'u da kuma yaudarar mutane a zaben jihar Ondo da za a yi
  • Kungiyar mai rajin tabbatar da adalci da cigaba ta fadi yadda wasu jam'iyyu suke raba abinci da fetur da makudan kudi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Ondo a gobe Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Wata kungiya mai rajin tabbatar da adalci ta zargi jam'iyyun siyasa a jihar Ondo kan yaudarar mutane.

Kungiyar JDPMC reshen jihar Osun ta ce akwai wasu jam'iyyu da ke ba da fetur da kudi da kuma abinci kan zaben Ondo da za a yi.

An zargi jam'iyyun siyasa da yaudarar mutane da kudi da fetur a zaben Ondo
Kungiya ta yi gargadi kan fara suyan mutane a zaben Ondo da za a yi. Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa, Ajayi Alfred Agboola.
Asali: Twitter

Ana zargin an fara siyan kuri'u a zaben Ondo

Kara karanta wannan

APC, PDP, da sauransu: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da siyasar jihar Ondo

Shugaban kungiyar, Rabaran Peter Akinkunmi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da The Guardian ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akinkunmi ya ce tabbas wannan zabe za a samu matsalar siyan kuri'u da sauran hanyoyin yaudarar mutane.

Ya ce kungiyarsu ta gano hakan ne bayan amfani da na'urar bin diddigi kan zaben yayin kamfe da ake yi a jihar.

Yadda ake jawo hankalin mutane a zaben Ondo

"Mun bi diddigi a dukan mazabu da yankunan da ake yin kamfen inda aka samu yawan ba al'umma kyaututtukan abinci da kuma kudade."
"Duba da yadda lamura ke tafiya, za a iya samun yawan siyan kuri'u da sauran hanyoyin yaudarar mutane su zabi wasu jam'iyyu daban."
"Mu na kira ga masu ruwa da tsaki da su yi yaki da masu siyan kuri'u domin tabbatar da ingancin zaben da za a yi."

- Rabaran Peter Akinkunmi

Ondo: INEC ta sauya dan takarar LP

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 game da zaben gwamnan jihar Ondo

Kun ji cewa Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta maido da sunan Dr. Olorunfemi Ayodele Festus a matsayin ɗan takarar gwamnan LP a zaben gwamnan Ondo.

INEC ta ɗauki wannan matakin ne bayan kotun ɗaukaka kara ta kori Olusola Ebiseni daga matsayin ɗan takarar LP tare da soke hukuncin kotun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel