Sakandare Kadai Su ka Kammala? 'Yan Takarar Gwamnan Ondo da Ke Neman Mulki da SSCE

Sakandare Kadai Su ka Kammala? 'Yan Takarar Gwamnan Ondo da Ke Neman Mulki da SSCE

A ranar Asabar 16 Nuwamba, 2024 ne yan takara daga jam'iyyun siyasa 18 za su fafata a zaben gwamnan Ondo, kuma kowace jam'iyya a cikinsu na fatan ta yi nasara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo - Manyan jam'iyyun da hankali ya fi karkata gare su su ne APC da PDP, sai jam'iyyun NNPP da LP da ake ganin za su tabuka wani abu. A cikin jerin yan takarar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta wallafa sunayensu, an gano da wasu sun yi rajista ne da shaidar kammala sakandare ne kawai.

Legit
Mutane 3 ne ke takarar gwamnan Ondo da shaidar Sakandare Hoto: Agboola Alfred Ajayi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro yan takarar da ke neman kujerar zaben gwamnan jihar Ondo da shaidar kammala Sakandare a wannan rahoton;

Yan takarar gwamnan Ondo masu shaidar SSCE

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Muhimman abubuwa 5 game da dan takarar PDP, Ajayi Agboola

Daga cikin ya takara 18 da hukumar INEC ta wallafa sunayensu, an gano uku daga masu neman kujerar gwamnan sun yi rajista ne da WSSCE ko NECO kadai, sun hada da;

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Ajayi na neman gwamna a PDP da SSCE

Jaridar The Nation ta wallafa cewa tsohon mataimakin gwamnan Ondo, Ajayi Alfred Agboola na daga cikin masu neman kujerar gwamnan jihar.

A jerin sunayen wadanda za su fafata a zaben Asabar, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar, Ajayi ya yi rajista da shaidar kammala sakandare ne kadai.

2. Emmanuel na ADP ya shiga zaben Ondo

Akinnodi Ayodeji Emmanuel ya na neman kujerar gwamnan jihar Ondo da takardar kammala sakandare, kamar yadda INEC ta wallafa. Akinnodi Ayodeji Emmanuel ya na takarar ne a karkashin inuwar jam'iyyar APD bayan an tsaida shi a watan Afrilu, cewar wani rahoton da Business day ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ondo: Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani kan Gwamna Aiyedatiwa da Ya Lashe Zabe

3. APP na takara a zaben gwamnan Ondo

Fadoju Amos Babatunde shi ne na tara a jerin wadanda INEC ta wallafa cewa su na neman zama gwamnan jihar Ondo. Mista Babatunde mai shekaru 56 da haihuwa ya na takarar a inuwar jam'iyyar APP, kuma shi ma ya tsaya neman zaben da takardar shaidar kammala sakandare.

Za a iya takarar gwamna da shaidar sakandare?

Dr. Sa'idu Ahmad Dukawa, fitaccen mai fashin bakin siyasa daga sashen kimiyyar siyasa na BUK ya ce dokar kasa ta kayyade shekaru da matakin ilimin masu takara.

Dr. Dukawa, wanda shi ne Sakataren zauren hadin kan malaman jihar Kano ya shaidawa Legit cewa babu banbanci tsakanin mai shaidar sakandare da mai sama da haka.

"... ya zama ya na da ilimi na matakin sakandare ko abin da ya ke daidai da hakan, "Wannan cewar abin da ya ke dai-dai da ilimin sakandare shi ne wanda mu ke bukatar fassarar masana," cewar Dr. Dukawa

Kara karanta wannan

APC, PDP, da sauransu: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da siyasar jihar Ondo

"Wannan shi ne ya ke da akwai, babu banbanci tsakanin kowane irin mukami ne, in dai na zabe ne mutum zai yi takara," in ji shi.

An tsaurara tsaro a zaben Ondo

A wani labarin kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya na cigaba da shirin tabbatar da an gudanar da zaben gwamnan Ondo a ranar 16 Nuwamba, 2024 cikin nasara.

Tuni rundunar sojojin ta aika dakaru masu yawan gaske zuwa Ondo domin taimakawa yan sandan da za su jagoranci tabbatar da tsaro kare jama'a a zaben.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.