Ondo 2024: Muhimman Abubuwa 5 game da Dan Takarar PDP, Ajayi Agboola
- Hukumar zabe a Najeriya (INEC) ta shirya gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo a gobe Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024
- Za a gudanar da zabe tsakanin yan takara daga jam'iyyu daban-daban da suka hada da APC da PDP da LP da SDP da NNPP
- Yayin da ake shirin gudanar da zaben a gobe Asabar, Legit Hausa ta yi duba game da abubuwa kan dan takarar PDP, Ajayi Agboola
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - A gobe Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024, za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo a karon farko bayan rasuwar marigayi Rotimi Akeredolu.
Daga cikin yan takarar akwai Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC wanda ke neman cigaba da zama kan karagar mulki.
Ondo: Abubuwa muhimmai game da dan takarar PDP
Sannan akwai dan takarar PDP, Ajayi Agboola wanda ya taba rike muƙamin tsohon gwamna a jihar, cewar rahoton ThisDay.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta yi bincike kan abubuwa muhimmai da ya kamata ku sani game da Ajayi Agboola da ke takara a PDP.
1. Haihuwar Agboola da karatunsa
An haifi Ajayi Agboola a ranar 24 ga watan Satumbar 1968 a kauyen Kiribo da ke karamar hukumar Ese Edo a jihar Ondo.
Agboola ya yi makarantar firamare a Kiribo inda ya kammala karatun sakandare a babbar makarantar Methodist a Okitipupa.
Daga bisani, Agboola ya samu digiri dinsa a Jami'ar Igbinedion da ke jihar Edo inda ya karanta bangaren shari'a.
2. Tushen siyasar Agboola
Ajayi Agboola ya shiga siyasa ne a shekarun 1980s a jam'iyyar SDP inda ya shugabanci gundumarsa tare da ba da gudunmawa mai tarin yawa.
A shekarar 1998, Agboola ya shiga jam'iyyar PDP inda ya samu damar rike mukamai daban-daban a matakin karamar hukuma.
3. Muƙamin mataimakin gwamnan Ondo
An zabi Ajayi Agboola mataimakin gwamna a karkarshin jam'iyyar APC a zaɓen shekarar 2016 da aka gudanar.
Agboola ya rike muƙamin ne karkarshin marigayi Rotimi Akeredolu daga shekarar 2017 zuwa 2021 a jihar.
4. Fadan Agboola da marigayi Akeredolu
A watan Yunin shekarar 2020, Agboola ya fice daga APC inda ya bayyana rashin jituwarsa da marigayi Rotimi Akeredolu wanda ya rasu a watan Disambar 2023.
Bayan komawa PDP, Agboola ya sha matsin lamba daga Akeredolu da APC domin ya yi murabus daga mukamin mataimakin gwamna, cewar Punch.
Sai dai Agboola ya ki amincewa inda ya maka su a kotu domin neman hakkinsa inda ya ce an zabe shi ne kan tsarin doka, ya ce zai cigaba da rike muƙamin tare da yin biyayya ga sabuwar jam'iyyarsa.
5. Zaman Agboola a Majalisar Tarayya
Hon. Ajayi Agboola ya wakilci mazabar Ilaje/Ese-Odo da ke jihar Ondo a Majalisar Dokoki ta Tarayya a birnin Abuja.
Yayin zamansa a Majalisar, Agboola ya jagoranci kwamitin raya yankin Neja Delta (NDDC) daga 2007 zuwa 2010 a matsayinsa na dan yankin.
Ajayi ya yi kokarin kawo sauyi kan tsarin yadda hukumar NDDC ke gudanar da ayyukanta domin inganta yankin Neja Delta.
Abubuwa muhimmai game da zaben Ondo
Kun ji cewa a gobe Asabar, 16 ga watan Nuwambar 2024, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Yan takara daga jam'iyyu daban-daban ke shirin karawa da gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa da yake jam'iyyar APC mai mulkin jihar.
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa a kan zaben jihar Ondo da za a gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng