Badaƙalar N1.3trn: Tsohon Gwamna Ya Faɗi Waɗanda Suka Turo Masa EFCC
- Abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2023, Ifeanyi Okowa ya ce zargin da EFCC take masa na karkatar da N1.3trn sharri ne da bi.ta da ƙullin siyasa
- Tsohon gwamnan jihar Delta ya bayyana cewa ya san mutanen da suka cinno masa EFCC don wata biyan buƙatarsu
- Okowa ya ce ba ya tsoron EFCC kuma ba zai hana hukumar gudanar da aikinta ba, yana mai cewa kudin da ake zarginsa a kansu sun zarce hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta - Tsohon Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce ya san mutanen da suka cinno masa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta fara bincikarsa.
Okowa, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP a 2023, ya ce ba ya jin tsoron duk binciken da EFCC za ta yi a kansa.
A cewar Daily Trust, Tsohon gwamnan ya faɗi haka a lokacin da ya karɓi bakuncin majalisar sarakunan jihar Delta a gidansa da ke Asaba ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Delta ya faɗa komar EFCC
Hukumar EFCC ta fara binciken Okowa, wanda ya shafe zango biyu a matsayin gwamnan Delta, kan zargin karkatar da zunzurutun kudi har naira tiriliyan 1.3.
A makon da ya gabata, EFCC ta tsare tsohon gwamnan bayan ya miƙa kansa a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Tsohon gwamnan ya bayyana zarge-zargen da ake masa a matsayin sharri da ƙagen siyasa.
EFCC: Tsohon gwamna ya zargi wasu mutane
Ifeanyi Okowa ya ƙara da cewa wasu mutane ne suke son jirkita gaskiya domin cimma wani burinsu na ƙashin kai.
"A siyasa akwai ƙalubale da dama da dole mutum ya fuskanta, amma abin da ciwo a rika yaɗa wasu zarge-zarge marasa tushe a kafafen watsa labarai.
"Ikirarin da ake cewa mutum ya saci irin waɗannan maƙudan kudi na nufin duk wata sai ya kwashi Naira biliyan 16 zuwa 20 har tsawon watanni 96, hankali ma ba zai ɗauka ba."
"Ba na tsoron EFCC" - Okowa
Dangane da tsare shi da EFCC ta yi a makon jiya, Okowa ya ce yana maraba da duk binciken da EFCC za ta yi kuma ba zai hana hukumar gudanar da aikinta ba.
Okowa ya jaddada cewa zargin da ake masa buta da ƙullin siyasa ne, inda ya kara da cewa cikin kwarin guiwa ya amsa dukkan tambayoyin jami’an EFCC, Punch ta kawo.
EFCC ta hana Okowa fita Najeriya
Mun kawo maku rahoton cewa hukumar EFCC ta karɓe fasfon tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa gabanin ta amince da bada belinsa.
Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun cafke Okowa ne bisa zargin karkatar da kudi da yake mulkin Delta.
Asali: Legit.ng