Zaben Ondo 2024: Cikakken Jerin 'Yan Takarar Gwamna a APC, PDP da Sauran Jam'iyyu

Zaben Ondo 2024: Cikakken Jerin 'Yan Takarar Gwamna a APC, PDP da Sauran Jam'iyyu

  • Masu kaɗa ƙuri'a na ta shirin fitowa domin zaɓen gwamna a jihar Ondo da ke yankin Kudu masu Yammacin Najeriya
  • Tuni hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana jerin ƴan takarar da za su fafata a zaɓen gwamnan
  • Zaɓen gwamnan dai na jihar Ondo an shirya gudanar da shi ne a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Akure, jihar Ondo - Za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo na shekarar 2024 a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba.

Gwamna mai ci na jam’iyyar APC, Lucky Aiyedatiwa na daga cikin waɗanda suka tsaya takara a zaɓen.

'Yan takarar zaben gwamnan Ondo
Lucky Aiyedatiwa da sauran 'yan takarar gwamnan Ondo Hoto: @A_AgboolaAjayi, @LuckyAiyedatiwa
Asali: Twitter

INEC ta bayyana sunayen ƴan takarar zaɓen Ondo

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa ƴan takara 18 ne za su fafata a zaɓen.

Kara karanta wannan

Ondo: INEC ta sanar da sakamakon rumfar zaben Gwamna Aiyedatiwa na APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin gwamna, Agboola Ajayi na jam’iyyar PDP na daga cikin waɗanda za su fafata da Aiyedatiwa.

Aiyedatiwa na jam’iyyar APC shi ne tsohon mataimakin gwamnan da ya zama gwamna, bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu a watan Disamban 2023.

Ajayi na jam'iyyar PDP ya kasance ɗan takarar gwamna na Zenith Labour Party (ZLP) a zaɓen 2020.

Jam’iyyun siyasa 18 da suka hada da APC mai mulki da ɗan takararta, Lucky Aiyedatiwa, Ajayi na PDP da sauransu za su fafata a zaɓen.

Jerin ƴan takarar gwamnan Ondo

Legit Hausa ta tattaro dukkanin ƴan takarar da jam'iyyunsu, kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar.

Duba su a ƙasa:

  1. Falaiye Ajibola (A)
  2. Akinuli Fred Omolere (AA)
  3. Ajayi Adekunle Oluwaseyi (AAC)
  4. Nejo Adeyemi (ADC)
  5. Akinnodi Ayodeji Emmanuel (ADP)
  6. Lucky Aiyedatiwa (APC)
  7. Popoola Olatunji Tunde (APGA)
  8. Ogunfeyimi Isaac Kolawole (APM)
  9. Fadoju Amos Babatunde (APP)
  10. Ebeseni Olusola (Labour Party)
  11. Olugbenga Omogbemi Edema (NNPP)
  12. Ajaunoko Funmilayo Jenyo (NRM)
  13. Ajayi Alfred Agboola (PDP)
  14. Ali Babatunde Francis (PRP)
  15. Akingboye Benson Bamidele (SDP)
  16. Adegoke Kehinde Paul (YP)
  17. Akinmurele John Otitoloju (YPP)
  18. Mimiko Olubamsile Abbas (ZLP)

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Dan takarar mataimakin gwamna na APC ya lallasa PDP a rumfar zabensa

Ƴan takarar gwamna sun koma bayan APC a Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa ana dab da zaɓen gwamna a jihar Ondo, ƴan takara uku sun janye daga zaɓen tare da marawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC baya.

Waɗannan ƴan takara sun fito ne daga jam’iyyun Accord Party, National Rescue Movement (NRM) da ADC, inda suka nuna gamsuwa da manufofin gwamnan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng