Ondo: Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani kan Gwamna Aiyedatiwa da Ya Lashe Zabe
- An gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 inda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaben
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa na daga cikin wadanda suka fafata a zaɓen da aka gudanar da sauran yan takara da dama
- Legit Hausa ta yi bincike kan dan Gwamna Lucky Aiyedatiwa takarar jam'iyyar APC domin kawo muku bayanai a kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - A ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 aka gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo a karon farko bayan mutuwar tsohon gwamna, Rotimi Akeredolu.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya gaji kujerar Akeredolu a Disambar shekarar 2023 na daga cikin yan takara da suka fafata a zaɓen domin neman nasara a karon farko.
Muhimman abubuwa kan dan takarar APC, Aiyedatiwa
Gwamna Aiyedatiwa ya dare kan kujerar mulkin ne a watan Disambar 2023 bayan rasuwar tsohon gwamna, Rotimi Akeredolu, TheCable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku abubuwan da ya kamata ku sani game da dan takarar APC, Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben da za a gudanar.
1. Shekaru da asalin Lucky Aiyedatiwa
An haifi Gwamna Lucky Aiyedatiwa a ranar 12 ga watan Janairun 1965 a kauyen Obe-Nla a karamar hukumar Ilaje da ke jihar Ondo.
PM News ta ce Aiyedatiwa ya yi makarantar firamare a St. Peters da ke karamar hukumar da kuma sakandare a babbar makarantar Ikosi da ke jihar Lagos.
2. Iyalan Lucky Aiyedatiwa
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya auri mace mai suna Oluwaseun Esther Aiyedatiwa inda suka haifi 'ya'ya uku tare a cewar rahoton Vanguard.
A 2023, an zargi Aiyedatiwa da cin zarafin iyalansa, lamarin da ya musanta inda ya ce iyalansa na daga cikin abin da ya fi ba muhimmanci a rayuwarsa.
3. Karatun digirin jami'a
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya fara karatu a Kwalejin ilimi da ke jihar Lagos wacce ta koma Jami'ar ilimi ta musamman a Ijanikin.
Aiyedatiwa ya yi karatun digiri a Jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo da kuma digiri na biyu a Jami'ar Liverpool da ke Burtaniya a 2013.
4. Kasuwancin Aiyedatiwa
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kware wurin harkokin kasuwanci inda ya bunkasa rukunin kamfaninsa na 'Blue Wall' tun 1996.
Rukunin kamfanonin sun hada da na canjin kudin kasashen ketare da na kula da jigilar jiragen sama a Najeriya.
5. Takarar dan Majalisar Tarayya
Lucky Aiyedatiwa ya nemi takarar dan Majalisar Tarayya a mazabar Ilaje/Ese-Odo a zaben 2015 da ya gabata karkashin jam'iyyar APC.
Aiyedatiwa ya tsunduma siyasa ne tun a shekarar 2011 karkashin jam'iyyar ACN kafin daga bisani a yi hadaka ta koma APC mai ci a yau.
6. Muƙamin kwamishina a NDDC
Lucky Aiyedatiwa ya rike muƙamin kwamishina a hukumar raya yankin Neja Delta domin wakiltar jihar Ondo da ke cikin jihohi masu arzikin mai.
Aiyedatiwa ya rike muƙamin kwamishinan Tarayya daga shekarar 2018 zuwa 2019 wanda ya ba shi damar kawo sauyi a yankin.
Gwamnonin Ondo tun daga 1999 zuwa yanzu
Kun ji cewa a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC na daga cikin yan takara da dama wadanda za su fafata a zaɓen da za a yi domin samun nasara a karon farko.
Yayin da ake shirin zaben a Ondo, Legit Hausa ta duba gwamnoni da suka mulki jihar daga 1999 zuwa shekarar 2024 da muke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng